Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Gwamnatin Jihar Zamfara ta kulla yarjejeniyar haɗin gwiwa da kamfanin XEJet Limited domin fara jigilar fasinjoji kai tsaye tsakanin Gusau da Abuja, inda ake sa ran fara zirga-zirgar jiragen sau biyu a mako daga wata mai zuwa.
An sanya hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) tsakanin gwamnatin jihar da kamfanin a ranar Litinin, a wani mataki da gwamnatin ta ce zai inganta sufuri tare da sauƙaƙa harkokin kasuwanci, zuba jari da yawon buɗe ido a Zamfara.
Wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce Mataimakin Gwamnan jihar, Malam Mani Mummuni, ne ya jagoranci bikin sanya hannu, yayin da Sakataren Gwamnatin Jiha, Malam Abubakar Mohammed Nakwada, ya sanya hannu a madadin gwamnatin jihar.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, XEJet zai fara gudanar da zirga-zirgar jiragen fasinja sau biyu a kowane mako tsakanin Filin Jirgin Sama na ƙasa da ƙasa na Gusau da Filin Jirgin Sama na ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Gwamnatin jihar ta ce sabuwar hanyar zirga-zirgar za ta inganta damar isa Zamfara tare da buɗe ƙarin damammaki ga masu zuba jari, ’yan kasuwa da baƙi.
Da yake jawabi a wajen bikin, Mataimakin Gwamna Mani Mummuni ya ce haɗin gwiwar ya yi daidai da manufar gwamnatin jihar ta inganta ababen more rayuwa na sufuri.
Ya ce an gina Filin Jirgin Sama na ƙasa da ƙasa na Gusau tun daga tushe, kuma aka kammala shi cikin shekaru biyu, da nufin sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki tare da taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Mummuni ya ce Gwamna Dauda Lawal na ci gaba da neman masu zuba jari na ƙasa da ƙasa da hukumomin bayar da tallafi da ke da sha’awar zuba jari a Zamfara.
Ya ce fara zirga-zirgar jiragen kasuwanci zai taimaka wajen jawo hankalin masu zuba jari, yayin da inganta hanyar shiga jihar zai samar da yanayi mai kyau ga bunƙasar kasuwanci da zuba jari.
