Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Sayyada Safiyya Sa’id, wadda aka fi sani da Tauraruwar Sarkin Baka ta Hausawan Afrika, ta shirya babban taron Maulidi a karon farko a farfajiyar ƙofar gidanta da ke birnin Kano a ranar Asabar da ta gabata.
An shirya taron ne domin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW), tare da tunawa da koyarwarsa da kuma ƙarfafa soyayya da bin ɗabi’un Manzon Allah (SAW).
Maulidin da Tauraruwar Sarkin Baka ta shirya ya samu halartar ɗimbin malamai manya da matasa, mawaƙa masu yabon Manzon Allah (SAW), da sauran bayin Allah salihai da masu kishin ganin an ƙara raya soyayya ga Annabi da kuma koyi da shi a halaye da mu’amalar yau da kullum.
Daga cikin malamai da suka halarci taron tare da gabatar da jawabai kan muhimmancin hidima da soyayyar Manzon Allah akwai Sayyadi Mudasir Zakari Mai ƙusa, wanda aka fi sani da Kamfani, kuma ɗan takarar Majalisar Wakilai ta Tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar ADP.
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Malam Bashir Bature Adam, Malam Abdulkadir Badawi da Alhaji Dayan, waɗanda suka bayyana farin ciki da muhimmancin taron Maulidi da kuma alherin da ke cikinsa bisa kyakkyawar fahimtar addinin Musulunci.
Haka kuma, taron ya samu halartar shahararrun mawaƙan yabo, ciki har da Sayyada Jamila Kurna, mai wakiltar Murja Hafizu Abdallah, da Alhaji Kabiru Dogarai, tare da sauran ɗimbin masu yabon Manzon Allah da addinin Musulunci.
Da take jawabi tun farko, Sayyada Safiyya Sa’id, Tauraruwar Sarkin Baka ta Hausawan Afrika, ta bayyana ranar Maulidin a matsayin rana mai matuƙar muhimmanci da farin ciki.
Ta ce ta ji daɗin shiga sahun masu yi wa Manzon Allah hidima ta hanyar shirya taron murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kuma raya koyarwarsa.
Ta kuma yabawa iyayenta, mijinta, ’yan uwanta na kusa da na nesa, da ɗaukacin mahalarta taron da suka nuna goyon bayansu ga wannan babban taro na Mauludi.
