Abin da Kwankwaso da Tinubu suka tattauna a ƙasar waje

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da ɗan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso a ƙasar Faransa.

Wata majiya mai tushe ta ce Tinubu ya yi wa Kwankwaso tayin tafiya tare da shi a sabuwar gwamnati da kuma duba yiwuwar sulhu tsakaninsa da Gwamnan Kano mai barin gado, Abdullahi Ganduje.

A ranar Litinin, mako biyu kafin Tinubu ya karɓi rantsuwar fara aiki, suka shafe sama da awa huɗu suna ganawar sirrin da Kwankwaso a birnin Paris na ƙasar Faransa.

Majiyarmu ta ce a yayin ganawar, Tinubu ya buƙaci haɗin kai domin aiki tare da Sanata Kwankwaso wanda ya lashe ƙuri’un Jihar Kano a zaven 2023.

Kwankwaso da shugaban ƙasar da ke jiran rantsarwa nan da mako biyu masu zuwa sun kuma amince za su ci gaba da tattaunawa kan wannan batu.

Majiyar ta ce mai ɗakin Kwankwaso da zavavven Sanata Abdulmumini na Jam’iyyar NNPP ne suka raka madugun Kwankwasiyya zuwa wurin ganawar.

A vangaren Tinubu kuma, matarsa, Sanata Oluremi da Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai mai barin gado, Femi Gbajabiamila, ne suka raka shi.

Majiyar ta ce “Matar Tinubu, Sanata Oluremi ce ta karɓi bakuncin Hajiya Hafsa, a yayin da ‘yan siyasar kuma suka ɗauki tsawon lokaci suna tattaunawa a kan haɗin kan ƙasa da abubuwan da sabuwar gwamnati za ta ba wa muhimmanci.

“Sauran sun haɗa da batun shugabancin Majalisar Dokoki ta Ƙasa da kuma aniyar zaɓaɓɓen shugaban ƙasan na kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa da ake fatan damawa da Kwankwaso a ciki.

“Sun kuma yi waiwaye a kan kawancensu na siyasa tun suna lokacin da suke Majalisar Dokoki ta Ƙasa a shekarar 19992,” in ji majiyar.

Majiyar ta ƙara da cewa a yayin zaman an kuma fara tunanin sasanta tsakanin Kwankwaso da tsohon mataimakinsa, wato Gwamnan Kano mai barin gado, Abdullahi Ganduje.

A shekarar 2015 Ganduje ya gaji kujerar Kwankwaso, amma ba da jima ba daga baya suka raba gari, kuma har yanzu ba sa ga-maciji.