
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kamfanin sadarwa na MTN a Nijeriya ya dakatar da tsarin bayar da bashin katin kira da data bayan gabatar da sabuwar buƙata da Hukumar kula da Gasa da Bada Kariya ga Kwastomomi (FCCPC) ta yi, wanda ke nuna an samu takura na bayar da rance a fagen dijital a ƙasar.
Rahotanni sun bayyana cewa babban kamfanin sadarwar ya bayyana haka ne a wata takarda da ya miƙa wa Kamfanin Canji na Ƙasa a ranar Alhamis, inda ya ce an dakatar da tsarin ne na wucin-gadi wanda ya zama wajibi sakamakon tabbatar da bin dokokin FCCPC, laturoni, da kuma na tsarin ba wa kwastomomi aro.
Tsarin, wanda ake kira da Xtratime, fage ne da masu amfani da layin da dama suke amfani da shi a Nijeriya domin karɓar rancen kuɗin kira ko data, inda suke biya yayin da suka sayi kati na gaba, wands mafita ne na gajeren zango ga miliyoyin masu amfani.
A saƙon, wanda Sakataren kamfanin, Uto Ukpanah ya fitar, MTN ya bayyana cewa, an soke tsarin a ƙarƙashin sababbin dokokin da aka kafa, waɗanda sun haɗa da tilasta ƙarin buƙatar wasu lasisi da bin hanyoyin da bin dokokin da masu bada bashin dijital suka samar.
Duk da wannan al’amari, MTN ya jaddada wa kwastomominsa cewa sauran shafukan sayen kati ko data sun cigaba da aiki yadda aka tsara, yana mai tabbatar musu da samun sabis mai ƙarfi a gare su.
