Matsin tattalin arziki: Kafar yaɗa labarai ta BBC za ta rage yawan ma’aikata 2,000

Spread the love

* Fiye da ‘yan Nijeriya 50 za su rasa aiki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gidan rediyo da talabijin na BBC ya sanar da shirin rage ma’aikata har zuwa 2,000 a duniya baki ɗaya, yana mai danganta hakan da matsin tattalin arziki da kuma sauye-sauyen da ke faruwa a fannin yaɗa labarai, lamarin da ka iya zama ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen tsarin aikinsa cikin kusan shekaru 15 da suka gabata.

A cikin wata sanarwa da aka aikawa ma’aikata ranar Laraba, mukaddashin Darakta Janar na BBC, Rhodri Talfan Daɓies, ya ce har yanzu ana duba cikakken tsarin, amma ana sa ran adadin ma’aikatan da za a rage zai kai tsakanin 1,800 zuwa 2,000. BBC, wadda ke da ma’aikata kusan 21,500, ta bayyana cewa wannan ragin zai shafi kusan mutum daya cikin goma na dukkan ma’aikatanta a duniya.

Ana sa ran wannan mataki zai yi tasiri sosai a nahiyar Afirka, inda BBC ta kara fadada ayyukanta a ‘yan shekarun nan. A halin yanzu, kamfanin na da ma’aikata kusan 600 a fadin nahiyar, inda cibiyarta mafi girma ke Nairobi da ke dauke da kusan ma’aikata 300.

Sai dai majiyoyi sun shaida wa News Point Nigeria cewa kusan ma’aikata 350 daga cikin wadannan na iya fuskantar rasa aikinsu. A Najeriya kuwa, ana sa ran sashen BBC Hausa—wanda ke daya daga cikin manyan kafafen yada labarai mafi tasiri—zai rasa kusan ma’aikata 54 daga cikin kimanin 93 da yake da su.

BBC ta ce wannan mataki ya zama dole ne saboda tana fuskantar “matsin tattalin arziki mai tsanani,” inda Rhodri Talfan Daɓies ya bayyana cewa “bambanci tsakanin kuɗaɗen shiga da kashe kuɗi na ƙaruwa.”

Ya kara da cewa dole ne kamfanin ya rage kashe kudi da fam miliyan 500 daga cikin kasafin kuɗinsa na fam biliyan 5 cikin shekaru biyu masu zuwa, tare da kokarin rage kashe kuɗi da kashi 10 cikin dari a cikin shekaru uku.

Wannan mataki ya jawo damuwa daga masu ruwa da tsaki a fannin yada labarai, inda kungiyoyin kwadago suka yi gargadin cewa hakan zai shafi aikin jarida da hidimar watsa labarai ga jama’a. Philippa Childs ta kungiyar Bectu ta bayyana matakin a matsayin “mai matukar muni,” yayin da Laura Daɓison ta kungiyar National Union of Journalists ta ce shawarar “ba daidai ba ce, kuma za ta jawo damuwa da rashin tabbas ga ma’aikata.”

BBC ta bayyana cewa wannan sauyi yana daga cikin kalubalen da ke fuskantar kafafen yada labarai a duniya, ciki har da bullar fasahar kere-kere ta zamani (AI) da kuma sauyin dabi’un masu sauraro.

Kamfanin, wanda galibin kuɗaɗen shigarsa ke fitowa daga kuɗin lasisin jama’a, ya ce kuɗaɗen shigar da yake samu sun ragu da kashi 24 cikin ɗari tun daga shekarar 2017, lamarin da ya kara tilasta daukar matakan rage kashe kuɗi. Haka kuma ya gargadi cewa karin ragi na iya haifar da rage wasu shirye-shirye da ayyuka.

Ragin ma’aikatan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen shugabanci da kuma ƙalubalen shari’a. Tsohon Darakta Janar, Tim Daɓie, ya sauka daga mukaminsa a farkon wannan wata bayan wata shari’ar ɓata suna da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya shigar dangane da wani shiri da ya shafi tarzomar Capitol ta 2021.

A halin yanzu, ana sa ran tsohon jami’in Google, Matt Brittin, zai karbi ragamar shugabancin BBC a wata mai zuwa, inda aka ɗora masa alhakin jagorantar kamfanin cikin wannan sabon yanayi na sauyi.

Yayin da BBC ke shirin aiwatar da wannan ragi, Rhodri Talfan Daɓies ya amince cewa matakin ba zai zama mai sauki ba, yana mai cewa, “akwai manyan shawarwari masu wahala da za a ɗauka,” lamarin da ke nuna girman ƙalubalen da ke gaban daya daga cikin manyan kafafen yada labarai na duniya.

By ukarofi