Zan dawo da aikin bututun iskar gas zuwa Kano — Dr. Fatah Zango

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Mai neman tsayawa takarar Sanata a jam’iyyar APC a Kano ta Tsakiya, Hon. Muhammad Musa Fatah Zango, ya bayyana cewa idan ya samu nasarar zama Sanata mai wakiltar yankin a zabe mai zuwa, babban abin da zai bai wa fifiko shi ne dawo da aikin janyo bututun iskar gas daga Fatakwal zuwa Kano.

Ya ce wannan mataki zai taimaka wajen farfado da masana’antu, tare da ba da muhimmanci ga bangarorin kiwon lafiya, ilimi da kuma noma.

Dr. Fatah Zango ya bayyana hakan ne a wani taro da ya gudanar a ranar Asabar da ta gabata a Kano, domin nuna aniyarsa ta tsayawa takara tare da zabo shugabannin da za su taimaka masa a tafiyar siyasa daga kananan hukumomi 15 na yankin.

Ya ce aikin bututun iskar gas din, wanda zai biyo ta Jihar Kaduna zuwa Kano, an fara shi shekaru da dama da suka wuce lokacin yana babban darakta a cibiyar magunguna ta kamfanin NNPC, amma daga bisani aka dakatar da shi.

A cewarsa, dawo da wannan aiki zai taimaka matuka, musamman ganin yadda masana’antu a yankunan suka durkushe sakamakon matsalar wutar lantarki. Haka kuma, zai bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga matasa.

Ya kara da cewa bangarorin noma, ilimi da lafiya na daga cikin manyan kudurorinsa, yana mai jaddada cewa ba za a samu ci gaban al’umma ba sai an ba wadannan fannoni kulawa ta musamman.

Hakazalika, ya ja hankalin wadanda aka zabo domin tafiyar siyasar da su yi aiki tukuru domin samun nasara, yana mai cewa su gode wa Allah da ya ba su wannan dama ta jagoranci.

Da yake jawabin godiya a madadin wadanda aka zaba, Zakariya Alkanawi daga karamar hukumar Garun Malam ya nuna farin ciki tare da tabbatar da cewa za su yi iya bakin kokarinsu wajen ganin dan takarar ya samu nasara, tare da yada manufofinsa a dukkan sassan yankinsu.

By ukarofi