Abin da ya sa Shettima ke wakiltar Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81 – Ministan Labarai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris Malagi, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilce shi ne a taron Majalisar Ɗinkin Duniya saboda yana halin hutun shekara.

Mohammed Idris ya ce, Shettima ya ɗauki cikakken umarnin Shugaban da Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya wajen wakiltar ƙasar a babban taron karo na 81, yana mai watsi da batun cewa rashin ganin shugaban ƙasar a taron ka iya rage ƙarfin martabar Nijeriya a harkokin difulomasiyya. Wannan bayani na zuwa ne bayan da Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar a hukumance cewa Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron UNGA na 81 a New York.

A sanarwar da ministan labaran ya fitar a ranar Litinin, ya ce, “a halin yanzu Shugaba Tinubu yana hutun shekara, kuma matakinsa na umartar Mataimakin Shugaban Ƙasa ya jagoranci tawagar Nijeriya ba sabon abu ba ne ko rage ƙarfin matsayin difulomasiyyar ƙasar.”

Tinubu ya buƙaci Shettima ya jagoranci tawagar Nijeriya a taron UNGA na 81 a New York, inda ake tsammanin mataimakin shugaban ƙasar ya gabatar da jawabin Nijeriya da kuma shiga muhimman hada-hadar tattaunawa tsakanin wakilan ƙasashe da harkokin da Nijeriya ta haɗu da wasu ƙasashe akansu.

A cewar Idris, ababen da Shettima zai shiga a dama da shi a cikinsu za su taimaka wajen fifita matsayar Nijeriya akan zaman lafiya da tsaro, ci-gaban tattalin arziƙi, matakan kula da yanayi, gyaran tsare-tsaren kuɗi a matakin duniya, ci-gaba mai ɗorewa da haɗin kai tsakanin ƙasashe.

Hakan na zuwa ne yayin da ‘yan ɓangaren suke sukar rashin halartar Shugaban Ƙasar a babban taron karo na uku a jere a daidai lokacin da ake cigaba da tunkarar babban zaɓen 2027. A ranar 30 ga Agusta, 2026 ne Shugaba Bola Tinubu ya fara hutunsa na shekara, wanda aka tsara zai shafe makonni uku kafin dawo wa harkokin mulki.

By Babaji

Leave a Reply