
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin Babbar Kotun Tarayya ta ɗaga sauraron ƙarar neman biyan diyyar Naira biliyan 1 da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya shigar akan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da wasu zuwa ranar 27 ga Oktoba.
Sauran waɗanda tsohon gwamnan ya shigar ƙara tare da ICPC sune Sufeto-Janar na Rundunar ‘Yan sanda (IGP) da Antoni-Janar na Ƙasa (AGF) a matsayin ɓangare na biyu da na uku.
Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ce ta ɗage shari’ar domin bai wa lauyan da ke kare tsohon gwamnan, Akinyemi Aremu damar bayar da amsa ga ƙorafin AGF da ke musanta iƙirarin.
A lokacin da aka kira domin sauraron ƙarar, Aremu ya shaida wa kotun cewa an shirya yin shari’a akan al’amarin. Lauya mai kare AGF, Maimuna Lami-Shiru a ɗaya gefen, ta shaida wa kotun cewa sun shigar da ƙorafin musanta ƙarar tsohon gwamnan. Ta roƙi kotun da ta amince wa buƙatarsu ta bayar da ƙarin lokaci domin gudanar da aiki akan ƙorafin nasu cikin tsanake kafin cigaba da sauraron ƙarar.
A sakamakon haka ne Alƙali Joyce ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 27 ga Oktoba, 2026.
El-Rufai ya shigar da ƙarar neman biyan sa diyyar ne a sakamakon abin da ya kira da “kai samame gidansa da yin bincike ba bisa doka ba” daga jami’an hukumar ICPC a ranar 19 ga Fabarairu.
