Adamu Aliyu ya zama sabon Shugaban ICPC

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Dr. Musa Adamu Aliyu a matsayin sabon shugaban hukumar yaƙi da rashawa ta ICPC gabanin Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin.

Kazalika, Tinubu ya Mr. Clifford Okwudiri Oparaodu a matsayin sakataren hukumar.

Bayanin naɗin na ƙunshe ne a cikin sanarwar da Kakakin Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Talata.

A cewar sanarwar, an naɗa Adamu Aliyu shugabancin ICPC ne domin maye gurbin tsohon shugaban hukumar wanda wa’adin shugabancinsa ya zo gab da ƙarshe.

Ta ƙara da cewa Dr. Musa Adamu Aliyu babban lauya ne wanda ya riƙe muƙamai da dama, ciki har da muƙamin Babban Lauyan Jihar Adamawa.

Haka shi ma Mr. Clifford Okwudiri Oparaodu lauya ne mai ƙwarewar aiki na sama da shekara 30.

Shugaba Tinubu ya buƙaci waɗanda naɗin ya shafa da su yi aiki tukuru babu tsoro babu tausayawa don sauke nauyin da ke kansu da kuma cigaban hukumar.