Kotu ta tsige ɗan Majalisar Wakilai daga Adamawa

Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta a Abuja ta tsige ɗan Majalisar Wakilai daga Jihar Adamawa, wato Hon. Jingi Rufai, na jam’iyyar PDP.

Kafin wannan lokaci, Jingi Rufai shi ne mai wakiltar Mubi ta Arewa, Mubi ta Kadu da Maiha a Majalisar Wakilai ta Ƙasa.

Kotun ta yanke hukuncin haka ne a zaman da ta yi a ranar Talata, inda ta bayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Hon. Jaafar Magaji, a matsayin wanda ya lashe zaɓe.

Kotun ta kuma bai wa hukumar zaɓe IMEC umarni a kan ta miƙa wa Magaji shahadar lashe zaɓen ba tare da wani jinkiri ba.

Wannan na zuwa ne bayan da kotun ta tsige sanata mai wakiltar Adamawa ta Kudu, Sanata Abbo daga kujerarsa a ranar Litinin da ta gabata.