‘Yan bindiga sun kashe jama’a da dama, sun yi awon gaba da wasu a Kano

‘Yan bindiga a Jihar Kano sun yi garkuwa da mutanen da ba a tantance yawansu ba kana sun kashe wasu a hare-haren da suka kai a yankunan Ƙaraye da Rogo a jihar.

Wani mazaunin yankin Ƙaraye da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa majiyarmu cewa, ‘yan bindigar sun kai hari yankin ne tsakanin Asabar da Lahadin da suka gabata kuma a lokuta daban-daban.

“An sanar da cewar a ranar farko da aka kai harin, kimanin mutum huɗu aka kwashe sannan mutum biyu sun mutu, yayin da a rana ta biyu aka sace mutum biyu tare da kashe wasu da dama.

“A bayyane yake cewa akwai buƙatar girke sojoji a Ƙaraye saboda hare-haren ‘yan bindiga,” in ji shi.

Ƙoƙarin da aka yi domin jin ta bakin Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ci tura.

Bayanai sun ce a lokutan baya-bayan nan yankunan Ƙaraye da Rogo na fama da matsalolin tsaro sakamakon kusancin Rogo da jihohin Katsina da Kaduna