Alamomin da mata ke ji da ke tabbatar da suna ɗauke da cutar sanyi

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barka da yau, barkanmu da sake kasancewa a shafin kwalliya na jaridar Manhaja. Har wa yau dai muna kan darasin ciwon sanyi, wanda idan ba a shafa’a ba, mun faro ne daga bayani kan ma’anonin da ake yi wa ciwon sanyi, zuwa bayyana adadi da karkasuwar ciwon.

A wannan satin da yardar mai dukka, shafin Kwalliya zai yi duba kan alamomin da mace za ta ji da za su iya tabbatar mata tana ɗauke da ɗaya daga cikin nau’ukan ciwon sanyi na mata. Hakan kuwa wata dama ce da za ta iya taimaka wa wurin saurin ɗaukar masa mataki tun bai kai inda zai iya yin babbar illa ba.

Ciwon sanyi ga mata, shi ne duk wani ciwo da zai tava walwalar farjin mace, ya hana shi sakewa tare da yin ababen da suke na al’ada a wurinsa. Hakan kuwa yakan haifar da damuwa da rashin walwala ga macen da ta ke tare da shi.

Ciwon sanyi kan iya zo wa da alamomi masu dama, waɗanda da yawa daga cikinsu ba su cika curarwa da za a iya saurin fahimtar su har a ba su taimako cikin gagawa, sai dai idan mace ta ajiye hankali sosai ne za ta iya fahimtar su.

Daga cikinsu akwai warin gaba, wanda da yawa a mata sai mazajensu sun kai ga ƙorafin ne za su ajiye hankalinsu wurin fahimtar shi. Sai kuma fitar ruwa daga farjin masu ƙamshi marar daɗi. Sau da yawa mata kan kasa bambance tsakanin waɗanda ke fita don ciwon sanyi da kuma sauran ruwan da mata ke fitarwa na sanayya. Hakan kuwa kan girmama lamarin kafin a san da shi.

Wani lokacin ma ciwon kan zo ne cikin sanɗa, ba tare da yin wata alama ba, wanda komai na farjin mace na tafiya yadda ya kamata kuma babu wani baƙon lamarin da ya ziyarce shi, sai dai hakan ba yana nufin ciwon bai same su ba, kuma ba yana nufin mace ba za ta iya fahimtar sa ba, sai dai sai ta ajiye hankalinta sosai ne ta ke iya gano hakan, ya Allah ta wurin walwalar ta, ko ta yadda ta ke jin wurin ba daɗi da sauransu.

A irin wannan an so mace ta kasance mai amfani da ‘yan kayan kawar da ciwon ingantattu waɗanda muke tu’ammali da su a rayuwarmu, ba kuma irin magunguna da ake haɗawa na Turawa ko gargajiya ba. Ina nufin tsakanin tsiro da muke ci ko sarrafawa yau da gobe.

Musali, kanunfari, abu ne da muke amfani da shi kusan kullum a rayuwarmu, sai dai kaɗan ne suka san za a iya amfani da shi wurin kawar da ciwon sanyi da bai yi ƙarfi sosai ba, kuma ana amfani da shi wurin ba wa farjin kariya daga kamuwa da ciwon na sanyi.

A wani vtangaren kuwa, alamomin sukan zo da takurawa ko ciwo da zai hana walwala, wanda suka fi saurin ankara da shi, misalin ƙaiƙayin gaba, wata alama ce da ciwon sanyi ma kan iya zowa da ita, duk da cewa, an fi haɗuwa da ita yayin da ya fara jimawa, duk da ana amfani da tsananin ƙaiƙayin wurin gane tsananin ciwon.

Akwai kuma zafin saduwa da wasu ke ji, ko in ce zafi a duk lokacin da wani abu ya shiga wurin komai ƙarancin shi. Na san mai karatu zai ce kenan bushewar gaba na rashin na’ima ma ciwon sanyi ne. Zai iya zama eh, zai iya zama a’a. Dalili kuwa shi ne, ciwon sanyin ma kan iya haifar da bushewar gaba, wanda shi kuwa zai iya zama sanadin zafin. Sai dai fa akwai matsalar rashin ni’ima mai zaman kanta da ke haifar da bushewar gaba, wanda bushewar ce ke zama silar zafin saduwa.

Matsalar fesowar quraje ba dalili a farjin mace ma na iya zama alama ta samuwar ciwon sanyi wadda ita ma kan iya kai ga haifar da babbar matsala har da zai iya haifar da matsalar yawan ɓari ko rashin iya ɗaukar juna biyu ma bakiɗaya.