Falasɗinawa 500 sun mutu sakamakon harin Isra’ila a Gaza

Rahotanni daga Falasɗin sun ce, ɗaruwan mutane ne suka rasa rayukansu a wannan Talatar sakamakon harin da Isra’ila ta kai kan yankin Gaza na Falasɗinu ta sama.

Bayanai sun ce mafi yawan hare-haren an kai su ne a kan wani asibiti da ke kula da waɗanda suka samu raunuka a wannan yaki.

Majiyoyin kiwon lafiya a Gaza, sun ce adadin waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon farmakin da Isra’ila ta kai a ranar Talata kawai ya kama daga 300 zuwa 500 ne.

An dai kai waɗannan hare-hare ta sama ne a kan asibitin al-Ahli da ke Gaza, inda dubban fararen hula suka samu mafaka, yayin da wasu ke jinya ko kuma kula da majinyata da suka jikkata a tsawon kwanaki kusan 12 da aka shafe ana wannan rikici.

Wasu bayanai kuwa sun ce, ko baya ga wannan asibiti, ruwan bama-baman da Isra’ila ta yi sun shafi wata makaranta mallakar Majalisar Ɗinkin Duniya, inda dubban mutane ke zaune a matsayin ‘yan gudun hijira, inda a can ma aka ruwaito cewa an samu asarar rayuka.

Da aka nemi jin ta bakinsa a game da waɗannan hare-hare, mai magana da yawun rundunar sojin Isra’ila, Daniel Hagara ya ce ba ya da tabbas idan har an kashe wannan adadi, amma za su yi bincike a kai.

To sai dai shugaban ofishin UNRWA da ke kula da ayyukan jinkai a Falasdinu, Philippe Lazzarini, ya ce ko baya ga hari kan makaranta mallakinsu, an kuma kashe mutane shida a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Maghazi da ke tsakiyar Gaza.