Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya tsige shugaban NAHCON ya maye gurbinsa da Jalal Arabi

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Alhaji Ahmad Alhaji Jalal Ahmad Arabi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) inda zai yi shekara huɗu a wa’adin farko.

Bayanin naɗin na ƙunshe ne a cikin sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Laraba.

“Sabon Shugaban na NAHCON, Alhaji Jalal Ahmad Arabi, zai shiga ofis ne a matsayin muƙaddashi a ranar 18 ga Oktoba, daga bisani ya zama cikakken shugaba na hukumar na wa’adin shekara huɗu farawa daga ranar 17 ga Janairu,” in ji sanarwar.

Ahmad Arabi ya gaji wannan kujerar ne daga Alhaji Zikrullah Kunle Hassan wanda zai tafi hutun gabanin yin murabus na wata uku.