Dalilin Sanata Ndume na ficewa daga zauren Majalisa a fusace

Da alama dai abubuwa ba su tafiya yadda ya kamata wa Majalisar Dattawan Nijeriya musamman ganin yadda shugabanin majalisar suka shiga ganawar sirri mintoci ƙalilan da fara zaman majalisar a ranar Talata.

Yayin zaman Majalisar a ranar Talata an ga Mai Tsawatarwa na Majalisar, Sanata Ali Ndume (APC Borno ta Kudu), ya yi ƙoƙarin nusar da Majalisar dangane da kurakuran da ake zargi Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya tafka ba tare da an yi gyara ba.

Kuskuren da Ndume ke nufi shi ne kan batun ƙudirin da Sanata Summaila Kawu (NNPP Kano ta Kudu) ya gabatar a majalisa kan buƙatar da ke akwai na tafka muhawara a kan batun sake buɗe iyakar Nijeriya da Nijar, ba tare da soma karanto taken ƙudirin ba.

Ndume wanda ya dogara da doka ta 51, ya buƙaci Shugaban Majalisar da ya bari a yi duk wata gyara da taso ko aka gano yayin da ake tsaka da zaman majalisa.

Ya ce, “Wannan dokar Majalisar Dattawan Tarayyar Nijeriya ne. Idan ana tsaka da zaman majalisa sannan aka gano wasu kurakurai dole a tsaya a yi gyara kafin a ci gaba,” in ji shi.

Sai dai bayan da Ndume ya ja hankalin majalisar kan buƙatar a yi gyara game da wasu kurakurai, sai Akpabio ya yi hanzarin katse shi inda ya ce ba a komawa baya bayan an yanke magana kan wani batu, kana ya ce ƙorafin Ndume bai karɓu ba.

Haka shi ma Sanata Sunday Karimi (APC Kogi ta Yamma), ya miƙe a majalisar don yi wa Ndume mubaya’a ta hanyar dogaro da wata dokar majalisar, shi ma Godswill Akpabio ya taka masa burki.

Lamarin bai tsaya nan ba, domin kuwa hatta Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Jibrin Barau, ya miƙe yayin zaman majalisar tare da dogaro da doka ta 16, wadda ta bada damar kowane sanata na iya jan hankalin majalisa don neman a gyara wani kuskure ko kuma sake waiwayar wani batu da aka rigaya aka tattauna a majalisar domin yin gyara.

Domin ƙarfafa kalaman Barau, Sanata Ndume ya sake miƙewa tare da jan hankalin majalisar ta dogaro da dokar majalisar ta 54, duka dai da nufin a tsaya a yi gyara kuskure.

A nan ɗin ma Shugaban Majalisar ya ƙi bai wa Ndume damar yin cikakken bayani game da ƙorafinsa, ya dakatar da shi.

Majiyarmu ta ce rashin jin daɗin matakin da Akpabio ya ɗauka hakan ya sa Ndume ya tattara takardunsa ya fice daga zauren majalisar a fusace.

Ganin abin da ya faru yayin zaman majalisar, hakan ya sa shugabannin majalisar shiga tattaunawar sirri, kamar yadda majiyarmu ta rawaito.