Yaƙin Isra’ila da Hamas: Tura ta kai bango

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Wani hoton bidiyo da na gani ya nuna wasu ƙananan yara mata suna la’antar wasu sojojin Isra’ila da ke cikin shirin yaƙi a wani yanki na ƙasar Falasɗinu da ke ƙarƙashin mamayar yahudawan Isra’ila, yayin da sojojin ke korar yaran su tafi gida. A gefe guda kuma ’yan jarida ne ke ɗaukar hotunan abubuwan da ke faruwa. Babu mamaki hakan ya sa sojojin kasa ɗaukar wani mataki a kan yaran. Amma abin da na lura da shi shi ne yadda yaran ke magana cikin fushi yana qara nuna yadda al’ummar Falasɗinu ke cike da fushi da damuwa kan danniya da zaluncin da ƙasar Yahudawan Isra’ila ke cigaba da nunawa a ƙasar su.

A bayyane yake cewa, Falasɗinawa sun kai maƙura kan irin abubuwan zalunci da suke fuskanta a wajen dakarun tsaron Isra’ila da munanan manufofin gwamnatin ƙasar da ke samun goyon bayan ƙasashen Turai, musamman Amurka, Ingila, Jamus da Faransa. Wani rahoto da ƙungiyar Save The Children ta fitar ya bayyana cewa fiye da rabin mutanen da ke rayuwa a wannan yanki na Zirin Gaza ƙananan yara ne da ba su san wani abu da ake kira zaman lafiya ko rayuwa cikin ’yanci ba.

Marubuci Sun Tzu da ya rubuta shahararren littafin nan na dokokin yaƙi, wato The Art of War, ya bayyana cewa, ‘Idan ka killace maƙiyanka ka hana su sakat, ka hana musu duk wata dama ta ’yanci to, idan fa tura ta kai su bango, za su fuskantoka da dukkan ƙarfinsu, kuma ba za su ja baya ba!’ Za a iya cewa wannan shi ne kuskuren da ƙasar Isra’ila ta yi wajen killace yankin Zirin Gaza da quntatawa Falasɗinawa da take yi fiye da shekaru 17, cikin ƙuncin rashin wadatattun magunguna, rashin ingantaccen ruwan sha, da makamashi.

Babu shakka harin ranar Asabar da mayaƙan Hamas suka kai cikin Isra’ila ta kusurwoyi daban-daban ya girgiza gwamnatin ƙasar da jama’arta waɗanda suka bayyana cewa tun kimanin shekaru 50 rabon da su ga irin wannan mummunan hari a ƙasar su, wanda a sanadiyyar haka an rasa rayukan Yahudawa da wasu baqi ’yan ƙasashen waje kimanin 1,200, banda asarar dukiya mai yawa da harin ya haifar.

A wani bidiyo da dakarun Hamas suka fitar ta kafar yanar gizo game da yadda suka suka kai wannan mummunan harin ramuwar gayya, da ba a taɓa ganin irinsa ba, an jiyo mayaƙan na magana cikin harshen Larabci irin na mutanen Gaza, suna ambaton sunayen ’yan uwansu da Isra’ila ta yi wa kisan gilla a yayin hare-haren da ta ke kai wa, suna cewa ‘wannan fansar ran ɗan uwana wane ne!’ ko ‘wannan fansar ran ɗana wane ne!’ Suna ambaton wasu zafafan kalamai na ɓacin rai da ƙuncin zuciya, cikin takaicin abubuwan da Isra’ila ta daɗe tana aikata musu.

Kodayake biyo bayan wannan harin, dakarun ƙasar Isra’ila sun mayar da mummunan martani kan Birnin Gaza, inda suka ɓarnata dukkan gine-ginen zirin mai girman kadada 365 da mutane miliyan 2 da dubu 300, gari mafi cinkoson mutane a duniya. A cikin kwanaki uku kacal Isra’ila da ke da ƙarfin soja da manyan makaman yaƙi, ta kashe Falasɗinawa 1,055, yayin da ta jikkata fiye da mutum 5,000. A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Falasɗinu ta fitar ranar Laraba da safe, ta ce, dubban mutane suna cikin wani mawuyacin hali na jinya, da rashin magunguna da jini, da rashin wutar lantarki. Sun kuma kira al’ummar duniya su tallafawa mata da ƙananan yara da ke fuskantar barazanar kisa daga luguden wutar da sojojin Isra’ila ke cigaba da yi musu. Bayan rasa dukkan abubuwan da suka mallaka, ciki har da muhallansu da wuraren kasuwanci da makarantu.

Wasu manazarta da suka tattauna da tashar talabijin ta Aljazeera sun koka da yadda hare-haren jiragen yaƙi da Isra’ila ke kaiwa cikin Gaza yana ƙarewa kan gidajen zaman jama’a, da kasuwanni har ma da asibitoci, maimakon su fuskanci mavoyar mayaqan Hamas ɗin, ko kuma su tunkare su gaba-da-gaba. Sai dai abin takaici mafi akasarin waɗanda ke mutuwa mata ne da ƙananan yara.

Wata sanarwa da ta fito daga hukumomin ƙasar Isra’ila an jiyo suna umartar jama’ar yankin da su fita su bar garin, yayin da ƙasar ke shirin tura dakarun soji fiye da dubu 300 cikin yankin, don kai samame gida gida da nufin zaƙulo duk wani ɗan Hamas da ke garin, da nufin shafe su daga doron ƙasa bakiɗaya. Duk kuwa da kasancewar Zirin na Gaza rufe yake daga sauran yankunan ƙasar Falasɗinu, da duniya bakiɗaya tsawon shekaru. Babu wanda kai tsaye zai iya cewa ga inda wannan rikici ya nufa, ga kuma iya tasirin da zai yi a siyasar duniya.

Cigaba da kai hare-haren jiragen yaƙi kan raunanan al’ummar Gaza, hantara da lalata musu gine-gine gami da zubar da jinin mata da ƙananan yara, ya tayar da hankalin kowanne Musulmi har ma da waɗanda ba Musulmi ba, saboda ganin halin ƙuntatawa, zalunci da kisan gillar da al’ummar Falasɗinawa ke ci gaba da fuskanta.

Rahotanni daga kafafen watsa labarai na duniya, sun bayyana cewa, ƙungiyoyin al’umma daban-daban suna ta shirya zanga zangar lumana da jerin gwano domin yin Allah wadai da ta’addacin gwamnatin Isra’ila a Zirin Gaza, ciki har da ƙungiyoyin Yahudawa masu sassaucin ra’ayi da ke nesanta kansu da addininsu da abin da suke cewa, siyasa ce da ke ƙara jawo musu baƙin jini da ƙyama a duniya.

Mu da muke wannan sashi na duniya muna bibiyar abubuwan da ke faruwa cikin ƙunci da vacin rai na ganin halin da raunanan jama’ar Falasɗinu ke ciki. Kodayake babu abin da za mu iya yi a kai da ya wuce mu jajenta musu kuma mu taya su da addu’ar ubangiji Allah Ya kawo musu ɗauki, kuma ya sakanta musu daga wannan zalunci da ake nuna musu. Wasun mu kuwa da ke mu’amala da shafukan sada zumunta na Soshiyal Midiya mun riƙa ɗora saƙonni na yin tir da Allah wadai ga abubuwan da ke faruwa a wancan sashi na duniya.

Matsalar rikicin Isra’ila da Falasɗinu ba matsala ce ta addini kawai ba, akwai siyasar duniya, danniya da lalacewar shugabanci, wanda mu ma kan mu ‘yan Nijeriya ƙalubalen da muke fuskanta kenan. Sannan haƙƙi ne na mutumtaka kowanne mai hankali ya nuna damuwa da mummunan zubar da jinin bayin Allah da kisan gillar da ke aukuwa da wasu bayin Allah raunana, da ke wani sashi na duniya, ba sai don zai amfanar da mu ta wata hanya ba. Duk da yake dai ni ba ƙwararre ba ne a wannan ɓangaren.

Za mu cigaba da zuba ido, da nazarin abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, tare da addu’o’in samun zaman lafiya a ƙasar mu da duniya bakiɗaya. Kuma ba za mu manta da gwagwarmayar mu ta cikin gida ta neman gwamnati ta ƙara tsaurara matakan tsaro domin daƙile ayyukan ‘yan bindiga masu satar mutane suna garkuwa da su ba, da kuma qara kiran a kuɓutar da ’yan matan Fugus, Dutsin-Ma, Sakkwato, da sauran sassan Nijeriya da ake cigaba da garkuwa da su, bayan sace su daga makaranta, inda suke neman ilimi.