Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, MƊD, Antonio Gutteres, a cikin jawabinsa na ranar kawar da talauci ta duniya, ya yi iƙirarin cewa, a wannan duniyar tamu mai cike da ɗimbin arziki, bai kamata Talauci ya yi ma ta katutu ba.
Gutteres ya ce, duk da ɗimbin arzikin cikin duniyarmu amma kusan mutane miliyan 700 ke fama da ƙalubalen rayuwa, inda suke rayuwa a ƙasa da dala 2.15 daidai da naira N2,000 a duk rana.
Sama da mutane biliyan ɗaya ne ke fama da matsananciyar rayuwa daga ƙarancin abinci, ruwa, lafiya da ilimi.
Akwai biliyoyin mutane da ba su da tsaftataccen muhalli, ayyukan yi, wurin kwana ballanta kuma samun ‘yancin zamantakewa.
A halin yanzu, duniyarmu tana fama da rikice-rikicen yaki, rikicin wariya na ƙara ƙamari – musamman kan mata da ‘yan mata.
Duk abubuwan da suka janyo koma baya ga ci gaban mu da tsanancin talauci, na da alaka da tsarin tafiyar da harkokin kuɗi na duniya wanda ya tsufa da kuma rashin adalci wanda ke hana ƙasashe masu tasowa tallafawa don kawar da talauci da cimma manufar shirin ‘yancin zamantakewa da kawar da talauci na MƊD (SDGs).
Kusan mutane miliyan 500 ne za su kasance cikin matsanancin talauci acikin 2030.
Wannan, sam ba a abin da za a sa ido ana kallo ba ne kawai, dole a yi wani abu.
A taron koli na SDG da aka yi a watan Satumba, shugabannin ƙasashen duniya sun amince da buƙatar yin garambawul ga tsarin hada-hadar kuɗi na kasa da kasa, tare da himmatuwa wajen yin wani kwakkwaran shiri don ceto muradun ci gaba mai ɗorewa da kuma kara kaimi wajen kawar da talauci a ko’ina.
Wannan ya hada da bayar da tallafi don ƙarfafa shirin SDG na akalla dala biliyan 500 a kowace shekara.
Shugabannin sun kuma amince da matakin da aka ɗauka da niyyar kawar da talauci da wahalhalun rayuwa ga dukkan mutane – daga tsarin samar da abinci da ilimi zuwa ayyukan yi masu nagarta da faɗaɗa kariyar zamantakewa.
