ADC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin soke jagorancin su David Mark da takarar Atiku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC) ta dauƙaƙa ƙarar hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta yi a kwanan nan, bisa rikicin shugabanci da ya haɗa jam’iyyar da Nafi’u Bala Gombe, inda ta roƙi Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da kada ta ɗauki wani mataki da ka iya ruɗar da Kotun Ɗaukaka Ƙara kan al’amarin.

Jam’iyyar ta kuma ce, ta shigar da ƙorafin neman dakatar da aiwatar da hukunci har sai an ji matakin ɗaukaka ƙarar, tana mai cewa wajibi ne INEC ta yi biyayya ga matakan shari’a. ADC ta bayyana haka ne ta bakin Kakakin Kwamitin yaƙin neman zaɓenta, Phrank Shaibu a wata takarda, ranar Juma’a.

A cewar sanarwar, an ɗauki wannan mataki ne kan hukuncin Babbar Kotun Tarayyar na ranar 5 ga Nuwamba, 2026 a wata ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/1619/2025 da ta haɗa Nafi’u Gombe da ADC. Ta ce, ta riga ta sanar da INEC kan matakin nata na ɗaukaka ƙara a ranar 6 ga Nuwamban da ƙorafin neman a jinkirta aiwatar da hukuncin.

Sannan, ta buƙaci hukumar da ta ƙaurace wa ɗaukar mataki kan al’amarin yayin da aka kai wa Kotun Ɗaukaka Ƙara ƙorafin hukuncin, tana mai cewa tana amfana ne da hukunce-hukunce da dokar ƙasa ta ba ta na ƙalubalantar hukuncin don haka ya dace a bar shari’a ta yi aikinta.

Akan haka ne ta kuma kirayi mambobinta, magoya baya da ‘yan Nijeriya da suka yarda da tsarin dimukraɗiyya da kwantar da hankali da kuma kasancewa masu ƙwarin-gwiwa duk da bijirowar al’amarin.

By Babaji

Leave a Reply