Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugabanin Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa, Afirka na ƙara zama nahiyar da ake samun fetur maras inganci kuma mai arha, wanda ba za a yarda da shi ba a Turai ko Arewacin Amurka.
Wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur ta Nujeriya (NMDPRA) ke yunƙurin samar da tsayayyen samfurin farashin man fetur a yankin.
Dangote ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin gabatar da jawabin sa na musamman a taron ‘West African Refined Products Pricing and Markets Deɓelopment Conference’ da aka gudanar a Abuja.
Dangote ya bayyana cewa, saboda ƙarancin iya tace mai a cikin gida na nahiyar, Afirka na shigo da sama da tan miliyan 120 na albarkatun mai a duk shekara, kan kuɗi kusan dala biliyan 90.
Yayin da yake yaba wa Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NNPC), saboda samar da ɗanyen mai a Nijeriya tun farkon samar da man har zuwa yau”, ya bayyana cewa kamfanin yana shigo da gangar ɗanyen mai tsakanin ganga miliyan 9-10 daga ƙasar Amurka da wasu ƙasashe. Ya ce, “A yayin da muke magana a yau, mu na sayen gangar ɗanyen mai miliyan 9 – 10 duk wata daga ƙasar Amurka da sauran ƙasashe. Dole ne in gode wa kamfanin NNPC da ya samar mana da wasu kayayyaki na ɗanyen man Nijeriya tun daga farkon fari har zuwa yau.”
Dangote ya ci gaba da cewa, duk da cewa tana haƙo kusan ganga miliyan 7 na ɗanyen mai a kowace rana, Afirka na tace kusan kashi 40 na ganga miliyan 4.3 da take amfani da su a kullum na cikin gida. Akasin haka, Turai da Asiya su na tace sama da kashi 95 na abin da suke samu.
“Saboda haka, yayin da muke samar da ɗanyen mai da yawa, har yanzu muna shigo da sama da tan miliyan 120 na albarkatun mai da aka tace a kowace shekara, muna shigo da fatara zuwa nahiyarmu,” inji shi.
Yayin da ba da tabbaci dgame da ƙarfin kasuwanni masu ‘yanci da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, Dangote ya jaddada cewa dole ne kasuwanci ya kasance mai tushe cikin inganci na tattalin arziki.
