Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya gargaɗi magoya bayansa cewa za su fuskanci tsananin wahalar tattalin arziki idan aka sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a shekarar 2027.
Ya bayyana cewa suna da zaɓi biyu ne kawai, su kada Tinubu a 2027, ko kuma su mutu da yunwa.
Amaechi, wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Ribas ne, ya faɗi hakan ne a ranar Laraba yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a birnin Fatakwal, a ziyararsa ta farko zuwa jiharsa bayan da ya shiga jam’iyyar ADC.
Amaechi ya nemi tikitin takarar shugaban ƙasa a zaɓen fidda gwani na APC a shekarar 2023, amma bai yi nasara ba, Tinubu ya yi nasara wanda daga bisani ya lashe zaɓen gaba ɗaya.
Bayan faɗuwar tasa, Amaechi ya zama daya daga cikin masu suka mafi tsauri ga Tinubu, yana bayyana cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ba ta cika alƙawuranta ba, kuma talauci da yunwa sun yi ƙamari a ƙasar.
Amaechi yanzu yana tare da wasu fitattun jiga-jigan ‘yan adawa a Nijeriya, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar; tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai; da kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a 2023, Peter Obi, don ƙalubalantar Tinubu a 2027.
A wani gajeren taron maraba da shi a jihar, Amaechi ya shawarci magoya bayansa da su fara shiri tun daga yanzu.
“Don Allah ku fara shirin 2027 daga yanzu. Kowa ya koma gida ya fara yin rijista. Za mu kafa kwamitoci a kowace ƙaramar hukuma, waɗanda za su zagaya kowane unguwa don tantance adadin masu goyon bayanmu.”
Wani bidiyo da ke nuna Amaechi yana jawabi ga magoya bayansa an wallafa shi a shafin Facebook.
Ya bayyana cewa jihar Ribas ta yi suna wajen “rubuta sakamakon zaɓe,” kuma ya gargaɗi cewa dole a kawo ƙarshen wannan ɗabi’a don kauce wa tafka maguɗi.
Amaechi ya kuma ja kunnen magoya bayansa da kada su riƙa fita suna cewa “sakamakon zabe an rigaya an rubuta su,” yana mai cewa hakan zai hana mutane fitowa su kaɗa ƙuri’a.
“Idan kuka bar su su yi maguɗi, to ku sani jiharmu Ribas ta yi suna wajen rubuta sakamakon zaɓe. Dole ne mu hana su. Suna ta ihu bayan sun gama maguɗi. Don Allah kowa ya koma gida ya fara wayar da kai, domin waɗannan mutane ne za su fito su kaɗa ƙuri’a.”
Ya kara da cewa:
“Abu ɗaya mara kyau da kada ku taɓa yi shine – kar ku ce an rigaya an rubuta sakamakon, domin hakan zai rage wa mutane ƙwarin guiwar fita kaɗa ƙuri’a. Idan ba mu kaka wannan gwamnati ba, to dukkanmu za mu mutu da yunwa.
“Yanzu haka ‘yan Nijeriya suna kuka da mulkin Tinubu a zangon farko. Ku yi tunanin irin wahalar da zamu shiga idan ya samu zango na biyu. To fa za mu mutu gaba ɗaya. Mutane na mutuwa kullum, ba saboda rashin lafiya ba, sai saboda yunwa.
“Su na shela a Abuja cewa mu mun ƙare, ba mu da kowa, kuma an gama da mu.”
