Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jami’an gwamnatin jihar Adamawa guda biyu sun gurfana a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Yola bisa zargin karkatar da kuɗaɗen da Bankin Duniya ya bayar domin gyara makarantun firamare da rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai Zaman Kanta (ICPC) ta gurfanar da waɗanda ake zargin, Pooona Samuel da Arama Davies Gyandi a ranar Laraba, 10 ga watan Yuli, 2025, a gaban mai shari’a Tijjani G. Ringin, inda ake tuhumarsa da laifuka huɗu da suka haɗa da haɗa baki, halasta kuɗaɗen haram, da kuma karkatar da kuɗaɗen al’umma ba bisa ƙa’ida ba.
A wata sanarwa da kakakin hukumar ICPC, Demola Bakare ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa waɗanda ake zargin sun yi aiki a matsayin jami’ai a shirin zuba jari na ilimi na jihar da ke ƙarƙashin ofishin Akanta Janar na jihar Adamawa har zuwa shekarar 2020, lokacin da ake zargin sun aikata laifin.
Hukumar ta ICPC ta ce, jami’an sun haɗa baki ne wajen karkatar da jimillar kuɗi Naira Miliyan 4.9 da Kwamitin Kula da Makarantu (SBMC) ya bayar wanda Bankin Duniya ya ware domin sake gina makarantu a yankunan da ‘yan tada aayar baya suka yi ɓarna.
“Ya kamata su san taɓa waɗannan kuɗaɗen almundahana ne,” inji Bakare, inda ya ƙara da cewa kuɗaɗen da aka wawashe an ajiye su a wasu asusu masu zaman kansu maimakon a mayar da su domin gyara makarantu.
A cikin ƙarar, kotun ta bayyana cewa waɗanda ake tuhumar sun mallaki kuɗi har Naira miliyan 2.4 da hukumar SBMC ta makarantar firamare ta Kwaja da ke Mubi ta Kudu ta biya, wanda aka biya a asusun Pooona Samuel. Daga cikin wannan adadin, an mayar da naira miliyan 1 zuwa Arama Daɓies Gyandi.
Wani tuhume-tuhume kuma ya zargi Samuel da karɓar naira miliyan 2.5 da hukumar SBMC ta makarantar firamare ta Mutuku da ke ƙaramar hukumar Hong ta mayar, wanda ya kawo jimillar kuɗaɗen da ake zargin a cikin shirin zuwa miliyan N4.9.
Hukumar ta ICPC ta ce, an gano waɗannan kuɗaɗe ne a asusun ajiyar banki na Zenith, UBA, da kuma bankin Unity, inda ta tabbatar da cewa duk kuɗaɗen tallafin ne.
Duk waɗanda ake tuhumar sun ƙi amsa tuhume-tuhumen da ake tuhumar su da su lokacin da aka gurfanar da su a gaban kotu.
