Sojoji sun ƙwace haramtattun wuraren tace mai 14, sun kama mutum 62 a Neja Delta

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Jami’an runduna ta 6 ta sojojin Nijeriya sun kama wasu mutane 62 da ake zargin ɓarayin mai ne tare da ƙwace sama da lita 350,000 na man sata a wasu jerin ayyuka da suka gudanar a yankuna huɗu na Neja Delta.

An gudanar da aikin na baya-bayan nan a cikin kwanaki huɗu a wani ɓangare na ci gaba da kai farmakin da sojoji ke yi na yaƙi da satar mai, fasa bututun mai, da kuma laifukan da suka shafi yankin.

Haka zalika, an wargaza wasu wuraren da ake tace mai ba bisa ƙa’ida ba, tare da katse hanyar samar da kayayyakin.

Muƙaddashin Daraktan hulɗa da jama’a na runduna ta 6 Laftanar Kanal Jonah Danjuma ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Fatakwal a ranar Lahadin da ta gabata kuma ya rabawa manema labarai.

Danjuma ya ci gaba da cewa, aikin tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro ya kai ga lalata haramtattun wuraren tace mai 14.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “An samu waɗannan nasarori ne ta hanyar ayyuka daban-daban da aka gudanar tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro, inda aka samu nasarori a faɗin jihohin Ribas Bayelsa, Delta, da Akwa Ibom tsakanin ranakun 14 zuwa 20 ga watan Yulin 2025.

“Ayyukan sun kai ga kama wasu mutane 62 da ake zargi da yin zagon ƙasa a fannin tattalin arziki, an lalata wasu wuraren tace mai guda goma sha huɗu, an kwace kwale-kwale guda biyar, da kuma kwace sama da lita 350,000 na man fetur da aka sata a yankin.

“A jihar Ribas, a kusa da wata rijiya da aka yi watsi da ita a Joinkrama 4 a ƙaramar hukumar Ahoada ta Yamma, sojoji sun lalata wasu haramtattun wuraren tace mai guda shida.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, wasu kayayyakin da aka ƙwato daga wurin sun haɗa da injin janareta, injin walda, da kuma tankoki da dama.

By ukarofi