Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya haɗe da iska sun yi ajalin mutum biyar sannan wasu 92 suka samu munanan raunuka a ƙananan hukumomi bakwai na jihar Yobe.
Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA) Dr Goje ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba a Damaturu.
Ya ce iftila’in ya shafi al’ummomi 48 ne a faɗin ƙananan hukumomin da lamarin ya faru.
Dr Goje ya kuma ce bala’in ya shafi gidaje 1,264, tare da raba mutum 5,022 da muhallansu.
Shugaban ya kuma ce hukumarsa tare da haɗin gwiwar ƙungiyar bayar da tallafi ta ƙasa da ƙasa ACF tare da tallafi daga ofishin kula da harkokin wajen Jamus (GFFO), sun raba kayan agajin ceton rai ga magidanta 566 a ƙananan hukumomin Fika da Potiskum da lamarin ya shafa.
Kazalika, ƙididdigar haɗin gwiwa ta hukumar ta SEMA da ACF suka fitar ta ba da fifiko ga iyalan da waɗanda wannan iftila’i ya fi shafa kai tsaye musamman waɗanda suka rasa gidajensu, da kayan masarufi, ko damar samun wani taimakon na tsafta.
Mohammed Liman Kingimi, na ƙungiyar ACF, ya tabbatar da ƙudurin ƙungiyar na ƙara ba da taimako bisa ga yadda buƙatun hakan suka taso.
Ya ce ƙungiyar na kuma shirye-shiryen ƙaddamar da tallafin abinci ga magidanta 566 don rage musu raɗaɗi.
Dokta Goje ya buƙaci waɗanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da shi yadda ya kamata sannan ya jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na kare al’umma masu rauni ta hanyar ɗaukar matakan gaggawa.
Ya kuma jaddada ƙudirin hukumar cewa kullum a shirye take wajen gudanar da ayyukanta kamar yadda ya dace.
