Afuwar fursunoni: Kullum fargar jaji ka ke yi, Atiku ga Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya caccaki Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan sabon jerin fursunonin da aka yi wa afuwa, inda ya danganta Shugaban ƙasar da fargar jaji, yana mai cewa “al’umma na kallon gwamnati wadda take yin aiki kafin ta yi tunani”.

Atiku, ta bakin mai magana da yawunsa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya ce matakin saka masu laifuka irin su ’yan safarar miyagun ƙwayoyi da masu garkuwa da mutane cikin jerin waɗanda aka yafewa abin kunya ne, ba hikima ba.

A baya dai, fadar shugaban ƙasa ta janye jerin farko bayan cece-kuce daga jama’a. Sai dai a sabon jerin da Kakakin Shugaba Tinubu, Bayo Onanuga, ya bayyana, mutum 140 ne suka amfana, ciki har da Maryam Sanda, inda aka mayar mata da hukuncin kisa zuwa zaman gidan yari na shekaru 12.

Shaibu ya ce, “Mun sake ganin gwamnati ba ta jagoranci, sai dai ta bi abin da ake cewa. Idan ba a yi ƙara-ƙara ba, mafiyawan masu garkuwa da mutane za su shaƙi iskar ‘yanci da alfarmar Shugaban ƙasa.”

Ya yi tambayoyi masu nauyi kan yadda aka shirya jerin: Waye ya tara jerin sunayen? Me ya sa za a saka masu aikata manyan laifuka? Ina Babban Lauyin Tarayya lokacin da aka shirya wannan?

Ya zargi gwamnatin Tinubu da yin mulki ta kai-da-kai, yana mai cewa, “Wannan ba hikima ba ce — abin kunya ce.”

Shaibu ya ƙara da cewa gwamnati ta rasa hangen nesa, tausayi, da kunya, yana mai kira da a fitar da cikakken jerin sunaye da laifukansu don a ga ainihin gaskiyar lamarin.

Ya ce, “Wannan janye hukunci gyaran fuska ne kawai.”

Sakamakon wannan mataki, jama’a da dama a soshiyal midiya da sauran wurare sun nuna damuwa, suna masu ganin yafiya ga manyan masu laifi abin tsoro ne wajen yaƙi da rashin tsaro a Nijeriya.

By ukarofi