Sojoji sun ƙwato dabbobi 70 a Katsina da shawo kan rikicin manoma da makiyaya a Sakkwato

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rundunar Sojin Nijeriya, dakarun Operation Fansan Yanma sun tabbatar da jajircewarsu wajen yaƙi da ‘yan bindiga da kuma shawo kan rikice-rikice a Arewa maso Yamma, inda suka ƙwato dabbobi fiye da 70 tare da maido da zaman lafiya a wuraren da aka samu rikici tsakanin manoma da makiyaya.

A Jihar Katsina, sojojin sun yi arangama mai zafi da ‘yan bindiga a ƙaramar Hukumar Bakori, inda aka dawo da awaki 70 da tumaki bayan da suka yi musayar wuta da miyagun da ake kyautata zaton mabiya ne ga Abaku Aiki — jagoran ‘yan bindiga da ya ƙi amincewa da tattaunawar zaman lafiya da aka ƙaddamar a baya-bayan nan.

An bayyana cewa maharan sun afka garuruwan Ganjar da Alhazawa da daren 25 ga Oktoba 2025, inda suka sace mutane da dama tare da tafka barna kan dabbobi. Sai dai bayan samun cikakkiyar bayanan leken asiri, rundunar sojin tare da sauran jami’an tsaro suka bi sawunsu har zuwa dajin Laila. Musayar wutar da ta biyo baya ta tilasta wa ‘yan bindigar barin dabbobin da suka sace kafin su tsere.

Rahotanni sun tabbatar da cewa duk awaki 70 din da wasu tumaki sun koma ga mazauna yankin, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin bibiyar waɗanda suka tsere da kuma ceto mutanen da aka sace. Rundunar ta kara tabbatar wa jama’a da cewa za ta ci gaba da sintiri da haɗa kai da sauran Hukumomin tsaro domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya.

A Jihar Sakkwato kuwa, sojojin sun yi gaggawar shiga tsakani, inda suka daƙile rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma Hausawa da makiyaya Fulani a ƙauyukan Karangiya da Danjawo na ƙaramar Hukumar Silame.

Rikicin ya kunno kai ne da safiyar Lahadi, bayan zarginsu da ƙetare alƙiblar kiwo da kuma mamaye gonaki. Zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tashin hankali kafin zuwan jami’an tsaro.

Aƙalla mutane tara ne suka ji rauni — manoma biyar da makiyaya huɗu. An sallami guda biyar bayan samun magani a Asibitin Silame, yayin da wasu uku ke ci gaba da samun kulawa a asibiti.

Bayan lamarin, shugaban ƙaramar hukumar Silame ya kira ganawar gaggawa da shugabannin al’umma domin samar da matakan da za su magance irin wannan rikici nan gaba. A halin yanzu, dakarun tsaro na ci gaba da sintiri da sa ido a yankin, kuma an tabbatar da dawowar natsuwa.

Rundunar Sojin Nijeriya ta jaddada ƙudirinta na kare rayuka da dukiyoyi, tabbatar da doka da oda, da kuma ƙarfafa rayuwa mai cike da haɗin kai da zaman lafiya a yankunan Arewa maso Yamma.

By ukarofi