Don kada Boko Haram ta jefa wa masu zanga-zanga bom Jonathan ya ƙi cire tallafin mai – Sanusi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan bai iya aiwatar da cikakken cire tallafin mai a 2012 ba ne saboda tsoron harin bama-bamai na Boko Haram kan masu zanga-zanga — ba wai saboda matsin lamarin jama’a kaɗai ba.

Sanusi, wanda a lokacin shi ne Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) kuma ya yi babban ƙoƙari wajen ganin an kawo ƙarshen tsarin, ya yi wannan bayani ne a taron Oɗford Global Think Tank Leadership Conference mai taken “Better Leader for a Better Nigeria”.

Ya ce, tsarin da ake kira tallafin mai a wancan lokaci ba tallafi ba ne kai tsaye, illa dai “hedge” da gwamnati ta ɗaura wa kanta, inda take alƙawarin biyan bambancin farashi duk lokacin da farashin ya tashi a kasuwar duniya — lamarin da ya haifar da gazawa da asarar kuɗaɗe.

A cewar Sanusi, “Gwamnati ta yi wa ‘yan Nijeriya alƙawarin cewa ba za su biya fiye da wani farashi ba duk tsawon lokaci, ko farashin ɗanyen mai ko na canjin kuɗi ya tashi. Wannan ba tallafi ba ne, hedge ne mara kariya wanda aka sani a fannin kasuwanci. Irin haka kullum yana kaiwa ga tashi a gaba.”

Ya ce, farashin danyen mai da ya tashi daga dala 40 zuwa sama da dala 140 da kuma tashin farashin canjin dala daga N155 zuwa kusan N300 ya tilasta gwamnati fara aro kuɗi don biyan tallafi — har ta kai ga ana aro don biyan bashin da aka aro tun farko.

Sanusi ya jaddada cewa idan gwamnatocin baya — musamman na Jonathan — sun tsaya kan matakin a wancan lokaci, to zafin da ake sha yau ya kasance ƙasa ƙwarai. “A lokacin mun yi hisabi a CBN, mun ga hauhawar farashi zai tashi daga 11% zuwa kusan 13%. Bai kai abin da ke faruwa a yau ƙwarai ba.”

Game da dalilin janye matakin a 2012, Sanusi ya ce tsoron harin ƙunar bakin wake ne ya sa Jonathan ya sassauta. “A lokacin akwai dubban mutane a tituna. Boko Haram na kai hare-hare. Idan kunar bakin wake ya tarwatsa wani taro ya kashe mutane da yawa, batun tallafi zai koma rikici na kasa.”

Sarkin ya kuma ce matsalar Nijeriya ba kawai shugabanni ba ne, sai dai tsarin da ba ya samar da rarrabe tsakanin shugaban ƙasa da talaka. “Ko ka ɗauko mutane daga titi ka sa su a Majalisa, ba lallai ka ga bambanci ba. Muna da masu ilimi a gwamnati, amma sukan manta iliminsu a bakin ƙofa.”

By ukarofi