Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sabbin bayanai sun bayyana a binciken da sojoji ke yi kan wani makircin hamɓarar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, yayin da aka ruwaito cewa jami’an leƙen asiri sun gano wasu kuɗaɗen da ake zargi da karkatar da su zuwa Naira bilyan 45 da aka gano a asusun da ke da alaƙa da Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC).
An yi zargin an raba kuɗaɗen ga mutanen da aka fallasa a siyasance kuma wasu daga cikin jami’an soji da ake tsare da su a halin yanzu kan wannan makirci, kamar yadda majiyoyin tsaro da dama suka tabbatar a ranar Laraba.
Wannan ci gaban ya zo makonni bayan da wani shafi a yanar gizo ya ba da rahoton cewa an kama jami’an soji 16, waɗanda suka haɗa da muƙaman Kyaftin zuwa Birgediya Janar, saboda shirin juyin mulki.
Dandalin yanar gizo ya danganta wannan makirci da aka yi da soke bikin cika shekaru 65 na ‘yancin kai na Nijeriya da gwamnatin tarayya ta yi.
Amma Hedikwatar Tsaro ta musanta wannan iƙirarin cikin gaggawa, tana mai dagiyar cewa an tsare jami’an ne saboda karya ƙa’idojin soja, ba wai yunƙurin juyin mulki ba.
Majiyoyin tsaro sun shaida wa wannan jarida cewa Hukumar Leƙen Asiri ta Tsaro (DIA) ta faɗaɗa bincikenta bayan gano ma’amaloli manya-manya da aka yi taransifarsu daga asusun NDDC kuma ana zargin suna da alaƙa da sojojin da aka tsare.
Lamarin ya haifar da bincike mai zurfi kan manyan ma’aikatan gudanarwa na NDDC, waɗanda tun daga lokacin aka gayyace su don yi musu tambayoyi.
“Wannan wani ɓangare ne na babban bincike na leƙen asiri kan motsin kuɗin jama’a,” inji wani babban jami’in tsaro.
An ruwaito cewa an bai wa tsohon Gwamnan Bayelsa kuma tsohon Ministan Man Fetur na Jiha, Cif Timipre Sylva, kuma aikin kariya na bakin teku wanda ya kai Naira biliyan 45 yana cikin ma’amaloli da ake sake dubawa. Masu bincike sun yi iƙirarin cewa wani ɓangare na kuɗaɗen ya isa ga waɗanda ake zargi da hannu a cikin shirin juyin mulkin.
Lamarin ya haifar da fargaba a cikin NDDC, inda jami’ai ke fargabar cewa binciken zai iya faɗaɗa zuwa cikakken binciken kuɗi.
Dul ƙoƙarin neman tsokaci daga mai magana da yawun Hukumar, bai yi nasara ba.
Ga Cif Sylva, an kuma ambaci sunansa a cikin binciken da ake ci gaba da yi. Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa jami’an leƙen asiri sun kai samame gidansa da ke Abuja a ƙarshen mako, inda suka kama ƙaninsa, Paga, Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Cikin Gida da kuma direbansa.
