2027: Farfesa Sani Haruna ya ƙaddamar da billboard da aka kafa masa a Keffi

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Nasarawa a zaɓen shekarar 2027 dake tafe a inuwar jam’iyyar APC, Injiniya Farfesa Sani Muhammad Haruna ya ƙaddamar da wani babban billboard da wata masoyiyar sa ta siyasa mai suna Maryam Zakari wace a kafi sani da Hajiya Tani ta kafa a unguwar Kan-korafi dake kusa da fadar mai martaba Sarkin Keffi a ƙarshen makon da ake ciki.

Da ya ke jawabi jim kaɗan bayan ya ƙaddamar da babban billboard ɗin, ɗan takarar Farfesa Injiniya Sasa Muhammad Haruna ya bayyana farin cikin sa game da karamcin inda ya yaba wa Hajiya Maryam Zakari dangane da ƙoƙarin ta da sauran al’ummar yankin baki ɗaya musamman ɗinbin magoya bayansa.

Yace tabbas wannan karamcin zai ƙara masa ƙarfin gwiwa na gani ya cigaba da tallafa wa al’umma.

Ya ƙara da cewa ya yanke shawarar fitowa zaɓen gwamnan jihar ne a inuwar jam’iyyar APC don tabbatar ya ɗora daga inda gwamna Abdullahi Sule zai tsaya musamman wajen gudanar da kyawawan ayyukan cigaba a duka fannonin rayuwa don kai jihar matakin na gaba.

Daganan sai ɗan takarar, Farfesa Injiniya Sani Muhammad Haruna yayi amfani da damar inda yace ga dukan alamu zuwa yanzu goyon baya da yake samu wurin al’ummar jihar baki ɗaya yana bashi yaƙinin zai iya cin zaɓen.

Tun farko da take jawabi wadda ta kafa billboard ɗin ga ɗan katarar, wato Hajiya Maryam Zakari wacce a ka fi sani da Hajiya Tani ta bayyana cewa ta ga ya dace ne ta kafa wa ɗan takarar wannan billboard bayan ta ga kyawawan ayyukan da ya daɗe yana gudanar wa al’ummar sa tun kafin yanzu.

Tace zuwa yanzu matasa da yara da kuma mata da dama sun amfana da ayyukan agaji da Farfesan ya daɗe yana aiwatar ba tare da nuna banbancin addini siyasa ko ƙabila ba inda ta buƙaci al’umma baki ɗaya su zo a yi tafiyar dasu.

Suma da su ke tofa albarkacin bakin su daban daban, wasu masu ruwa da tsaki kuma na kusa da ɗan takarar da suka haɗa da Fasto Benjamin Baka da Alhaji Iyal Yakubu da kwamaret Muktar Sai’d duk sun yaba wa hangen nesa na wacce ta kafa billboard ɗin ta yi, inda suka ce basu yi mamakin matakin na ta ba idan a kayi la’akari da sadaukarwa da kuma aiki tuƙuru da yake yi don cigaban al’ummar sa ba dare ba rana.

Abubuwa da aka gudanar a yayin babban taron sun haɗa da ƙaddamar da billboard ɗin da ɗaukan hotuna sannan su kuma ana su ɓangaren makaɗa da maroƙa sun nishaɗantar da mahalarta taron.

By ukarofi