
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsige ɗan Majalisar Wakilai, Abubakar Gummi kan sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Ɗan majalisar shi ke wakiltar mazaɓar Gummi/Bukkuyum ta tarayya daga Jihar Zamfara.
Da yake gabatar da hukunci, Alƙali Obiora Egwuatu ya haramta wa Kakakin Majalisar Wakilan, wato Tajudeen Abbas cigaba da ɗaukar Abubakar Gummi a matsayin mamba a majalisar.
Haka kuma, Mai Shari’ar ya umarci hukumar zaɓe, INEC da ta shirya gudanar da sabon zaɓe acikin kwana 30 domin cike gurbinsa.
Jam’iyyar PDP da Shugabanta na jihar, Jamilu Jibo-Magayaƙi ne suka shigar da ƙarar bayan sun zargi ɗan majalisar da watsa musu ƙasa a ido duk da cewa PDP ce ta ɗauki nauyinsa har ya ci zaɓe a lokacin da babu rarrabuwar kai acikinta.
Haka kuma, ya ƙaƙaba tara akan wanda aka shigar ƙara na N500,000, kuɗaɗen da zai biya ɓangaren da suka shigar da shi ƙara.
