Rundunar ƴan sanda ta ƙasa a ranar Litinin ta bada sanarwar ladan miliyan N20 ga duk wanda ya bada bayanai in da za sami ɗan ƙasar Birtaniya Andrew Wayne da Lucky Ehis Obiyan kan zargin ɗaukar nauyin ta’addanci a cikin Nijeriya.
Wannan sanarwa na ɗauke ne a wata sanarwa ta musamman da rundunar ta fitar ga ƴan jarida a hedikwatar rundunar da ke Abuja.
” Duk wanda ya gansu, ya miƙa su zuwa ofishin ƴan sanda mafi kusa ko kuma ya kira lambobi kamar haka “08035179870, 09133333785, 09133333786.
Da yake magana da ƴan jarida, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ACP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana shima binciken da ake wa ƙungiyar ƙwadago ya haɗa da rashin sanin wanda ke zaune a cikin ginin na su. Ya ciga da cewa ɗan Birtaniyan ya fara shirin kifar da gwamnati ne ta hanyar biyan wasu kuɗaɗe ga mutane domin tada fitina da zai janyo ƙasashen duniya su yi wa gwamnatin tofin Allah tsine.
