Alamomin da ke nuna rashin wadataccen ruwa a jiki

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Mai karatu barkan mu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Muna godiya da jimirin bibiyar mu da ku ke yi.

A wannan makon za mu tattauna ne kan muhimmin abu da jiki ba ya iya rayuwa sai da shi, kuma rashin nasa babbar illa ce da ka iya haddasa wasu cututtuka manya da ƙanane. Ba kuwa komai na ke magana kai ba face ruwa.

Na san wasu za su yi mamakin jin rashin isasshen ruwa a jiki zai iya haifar da cuta ga jiki, kasancewar ba su ɗauke su a matsayin komai ba face abin kawar da ƙishirwa.

To mai karatu, ka ajiye hankali ka fahimci wannan darasi namu, matuƙar dai kana bisa wannan aƙida. Jikinka na buƙatar ruwa koda ba ka jin ƙishirwa. Za ka sha ruwa a lokacin da ka ke buƙatar shan, da kuma lokacin da ba ka yi muradin yin hakan ba, ba kuwa don komai ba face ganin ka wadata jikin da adadin da yake buƙata.

Matsayin ruwa a jikin ɗan adam ba abu ne na wasa ba, domin ya na buƙatar ruwa don gudar da al’amuran yau da kullum. Rashin su kuwa babbar illa ce da ka iya haifar da matsaloli da dama.

Sanannen abu ne, rashin ruwa na haifar da matsala a fata, saidai kaɗan ne suka san ba a iya fata rashin ruwa ke taɓa wa ba. Rashin shan ruwa yadda jiki ke buƙata, ko rashin ruwa a jiki kan iya haifar da curuta irin ciwon kai, rashin saurin narkewar abinci, da bushewar fata da ka iya haddasa tsagewar ta, da sauransu.

Haka kuma, idan rashin ruwa a jiki ya kai ƙololuwa zai iya haifar da manyan cututtuka kamar tsakuwar ƙoda, matsalar fitsari da sauransu.  Don haka yake da matuƙar muhimmanci shan ruwa akai-akai musamman ma a lokutan zafi wanda ruwan jiki ke saurin ƙonewa.

Duk da cewa ba a lokacin zafi ne kawai ya kamata a mayar da hankali kan shan isassun ruwa ba, domin ko a tsananin sanyi jiki na buƙatar ruwa, saidai ba kamar lokacin na zafi ba.

Ta yaya za ka iya gane jikinka ba ya samun isasshen ruwa?

By ukarofi