Biyo bayan zanga-zangar da a ka gudanar a faɗin ƙasa satin da ya wuce, a inda wasu wurare ta rikiɗe ta koma rikici. Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa, wasu ɓatagari da suka shiga babbar kotun jihar sun yi awon gaba da takardun da ake tuhumar tsohon gwamna, Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ne ya faɗi haka a yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai harabar kotun domin ganin irin ɓarnar da aka yi. Tare dashi akwai Kwamishinan Shari’a, Bar Haruna Isa Dederi da wasu manyan ma’aikatan kotun.
Sannan a wata sanarwar da ya fitar ta hannun mai magana da yawunshi, Sanusi Bature Dawakin Tofa, gwamnan ya bayyana lamarin a mastayin shiryayyen al’amari da ke son kawo cikas ga shari’ar tsohon gwamnan.
Daga ƙarshe yayi kira ga matasa da su guji bari a yi amfani da su wajen tayar da tarzoma, domin gudun abin da zai faru da kuma yin kira da matasa su kama sana’a domin ta wannan hanyar ce za su dogara da kan su domin gwamnatin shi na ba ɓangaren matasa muhimmanci sosai.
