Zanga-zanga: Me muka koya?

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Duk lamuran rayuwa na tafiya da hagu ko da dama da riba ko da asara. Hakan ya sa masu nazari kan zauna su yi lissafin kowanne bangare daga biyun wannene ya fi zama a’ala don ba da shawara ko ɗaukar matakai na gaba don rungumar abun da ya fi zama a’ala. Allah ya taimake mu ta mu zanga-zangar aƙalla a yanzu ba ta ɗau tsarin asarar da a ka yi bisa ƙarin farashin burodi a Sudan ba ko zugar ƙin jinin marigayi Mo’ammar Ghaddafi a Libya.

Ga ma tunzurin wasu ƙasashen Larabawa da ma kwanan nan yadda a ka yi gagarumar zanga-zanga Kenya da ta so kifar da dimokraɗiyyar ƙasar. Irin ta mu zanga-zangar ta samu cikas daga wasu baƙaƙen wake masu ata miya waɗanda su ka lalata dukiyar gwamnati da ta jama’a. Kazalika an samu asarar rayuka da har yanzu ba za a iya tantance alƙaluman yawan su ba duk da ‘yan sanda sun yi magana. A nan mu na addu’ar samun maida gurbi ga waɗanda su ka yi asara da miƙa ta’aziyya ga waɗanda su ka rasa ‘yan uwan su.

A zahiri ba amfanin baɗi ba rai duk da na ga wasu na zaiyana zanga-zangar da cewa gwagwarmaya ce kuma ai ba a nasara a irin wannan yanayi ba tare da samun asara ba. Gaskiyar magana sai mun yi adalci wajen ƙasa gwagwarmayar tsakanin masu da’awar yaƙi da yunwa da kuma masu gwagwarmayar sace kayan jama’a. Ba na tsammani akwai riba daya da a ka cimma zuwa yanzu na sauyi daga wuya zuwa dadi a sanadiyyar zanga-zangar nan. Kazalika tamkar a arewa ne yajin zanga-zangar ya fi zafi don haka gwagwarmayar ta wasu angarori ne ba dukkan ƙasa ba. Tsakani da Allah kowa ya cire hushi a zuciyar sa ya zauna ya yi dogon nazari kan riba ko akasin haka na wannan gwagwarmayar. Kafin nan za mu duba muhimman labaru da su ka biyo bayan fara zanga-zangar.

Zanga-zangar da matasa su ka fara gudanar da zummar yaƙi da kuncin rayuwa ta juye zuwa fitina a sassan Nijeriya.

Haƙiƙa an yi zaton masu shirya zanga-zangar sun janye zuwa wani lokaci amma sai a ka wayi gari a manyan garuruwan arewacin Nijeriya matasa sun yi dafifi kan tituna don zanga-zanga.

Kamar yanda a ka yi hasashe ba a kwashe lafiya ba don wasu miyagun iri sun kutso cikin zanga-zangar inda su ka riƙa fasa wasu gine-gine da satar dukiya.

Duk ƙoƙarin jami’an tsaro na hana satar abun bai yi nasarar da a ke buƙata ba a irin birnin Kano da Gombe da sauran su.

Tuni gwannatin Kano ta ayyana dokar hana yawo dare da rana don hana cigaba da arnar da ata gari ke yi duk yanzu an sassauta dokar.

A Abuja ma masu zanga-zanga da su ka ƙetare babban filin wasa zuwa cikin gari sun yi arangama da ’yan sanda da ke harba hayaƙi mai sa kwalla.

Shugaban JIBWIS Imam Abdullahi Bala Lau ya buƙaci matasa masu zanga-zanga su dakatar da zanga-zangar da su ka fara haka nan.

Matasan dai sun fara zanga-zangar kamar yadda su ka ayyana a ranar 1 ga watan nan na Agusta da niyyar cigaba har tsawon kwana 10.

Sheikh Bala Lau ya nuna juyayin yadda zanga-zangar ta juye zuwa shigowar wasu matasa masu mummunar manufa da su ka sace dukiyoyin jama’a.

Malamin ya ce duk dukiyar da a ka rasa da mutanen da su ka rasa ran su jama’ar arewa ne da ya dace a haɗa kai wajen yin nazarin samun mafita tare ba kara tsananta ƙalubalen ba.

Shehun malamin ya ce malamai a matsayin su na wakilan al’umma ba za su yi kasa a gwiwa wajen cigaba da isar da ƙorafin jama’a ga gwamnati har sai da yardar Allah an samu sauyi mai gamsarwa.

Sheikh Bala Lau ya yi addu’ar samun sauƙi ga al’umma da nuna zaman lafiya shi ne matakin samun nasara don zanga-zanga kan buɗe kafar da fitina za ta shigo ne da ba a san waye tsautsayi zai aukawa ba.

Datse babban titin da ya haɗa yankin Abuja da Kaduna da matasa su ka yi ya haddasa gagarumin tsaikon motoci na tsawon lokaci.

Matasan masu zanga-zanga na neman nuna fushin su ne ga tsadar rayuwa amma hakan ya kare kan matafiya.

Hanyar dai ita ce fitacciya da ta haɗa yankin arewa ta tsakiya da kuma yankin arewa maso yamma da ya fi yawan jama’a a Nijeriya.

Mutane sun tsaya cirko-cirko ba wata mafita don yadda hanyar ta cunƙushe ba shiga ba fita.

Ba bakon abu ba ne datse hanyar kuma hanyar ba ta gama farfadowa daga hare-haren masu satar mutane ba.

Jami’an tsaro sun yi amfani da albarusai kan masu gudanar da zanga-zangar yaki da kuncin rayuwa a Abuja.

Akasin ya auku a filin wasa na birnin da a ka radawa Moshood Abiola inda hakan ya kawo firgici.

Tun gabanin nan ma ‘yan sanda sun harba hayaki mai sa kwalla kan masu zanga-zangar don tawrwatsa su.

Hatta ‘yan jarida ba su tsira daga buɗe wuta na jami’an tsaron ba amma dai zuwa yanzu ba a samu labarin asarar rai ba sai dai lalata gilasan wata motar manema labarun.

Hukumar Abuja ta nemi killace masu zanga-zangar a iya filin wasan da ya ke gefen tsakiyar birnin.

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta ce sam ba ta kashe ko mutum ɗaya ba a zanga-zangar da matasa ke yi a sassan Nijeriya.

Wannan na ƙunshe a sanarwa daga kakakin rundunar Muyiwa Adejobi a dandalin rundunar na ɗ.

ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta AMNESTY ta zargi jami’n tsaron da kashe masu zanga-zanga 13.

A nan rundunar ta ce ba kamar yadda AMNESTY ta ce mutum 13 ne su ka mutu ba, mutum 7 ne kuma kutsowar ’yan ta’adda ne, ‘yan banga da wani direba mai tuƙin ganganci ya haddasa asarar rayukan.

Rundunar ta ce a Borno mutum 4 su ka mutu yayin da 34 su ka samu munanan raunuka sanadiyyar kutsowar ‘yan ta’adda  da su ka dasa boma-bomai a cikin ‘yan zanga-zangar.

Malaman Islama sun ce abun da a ka gani zuwa yanzu a fagen zanga-zanga shi ne abun da su ke jan hankalin matasa su kauce ma sa.

Musamman a huɗubar Juma’ar makon jiya, malaman sun ce sun hango za a samu miyagun iri su kutso cikin zanga-zanga don sace dukiyar jama’a.

A nan malaman sun ce maimakon samun maslaha, zanga-zangar ta ƙara ta’azzara ƙuncin da a ke ciki ne har ma da samun asarar rayuka.

Malaman sun yi kira ga matasan su dakatar da zanga-zangar haka don ba wata riba da za a cimma sai kara haddasa baƙin ciki da asara.

Wasu miyagun matasa sun shiga zanga-zangar a sassa daban-daban na Nijeriya inda su ka sace kayan jama’a ciki har da makara a wani masallaci.

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa ta tura biliyoyin Naira ga jihohi don taimakon jama’a.

Shugaban ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar ga ƙasa da a ka yada ta kafafen labaru a ranar Lahadi.

Bola Tinubu na bayyana matakai ne da gwamnatin sa ke ɗauka don kawo sauƙi ga ƙorafin jama’a da ya kai ga wasu matasa sun ƙaddamar da zanga-zangar yaki da yunwa.

Tinubu ya buƙaci matasan su dakatar da zanga-zangar su ɗau zabin tattaunawa da gwamnati.

Shugaban wanda ya nuna rashin jin daɗi ga yadda a ka  samu asarar rayuka da dukiyar jama’a a zanga-zangar amma bai yi magana kan zargin jami’an tsaro sun rutsa da sashen masu zanga-zanga cikin lumana ba.

ƙungiyoyin da ke jagorantar zanga-zangar yaƙi da kuncin rayuwa a Abuja sun lashi takobin cigaba da zanga-zangar har sai sun cika kwana 10.

Zanga-zangar wacce ta fara a sassan Nijeriya ranar Alhamis ɗin makon jiya ta haddasa asarar rayuka da dukiya.

Masu zanga-zangar dai na bayyana azamar sake isa babban dandalin taruka na EAGLE da ke daf da sakatariyar taraiya, majalisar dokoki, ƙotun ƙoli da fasar Aso Rock.

Kwamared Nasir Kabir na ƙungiyar ƙwadago NLC da ke jan ragamar wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ya ce ba su gamsu da jawabin shugaba Tinubu da ya ke kiran dakatar da zanga-zangar ba “mun ja hankalin jami’an tsaro wannan zanga-zanga ta lumana ce, ka da wani ya yi amfani da ikon sa ya ce zai musgunawa wani memban mu don ba za mu kyale ba.”

Murtala Garba da ya zama na farko da ya janye daga zanga-zangar ya ce abun da su ke hasashe na zagon ƙasa ga arewa ne ya auku “’yan kudu akwai wani rawa da su ke yi sai su jefa kafa baya, lokacin da a ka kashe Sardauna Ahmadu Bello da su Tafawa Balewa da sauran su, wannan da ya yi waƙar nan a na zolayar ‘yan arewa ne. An dawo da wannan wakar ɗin”

Sheikh Abdullahi Bala Lau da ya jagoranci tawagar malamai wajen ganawa da shugaba Tinubu kan ƙorafin matasan ya buƙaci su dakata haka nan “ Allah ya sani su ma jama’a sun gani mun yi abun da mu ke iyawa don mu isar da wannan saƙo. Mun nuna damuwar jama’a da halin da a ka samu kai. To idan sun yarda mu ne wakilan su to ai ya kamata in mun miƙa wannan saƙo al’umma su ƙara haƙuri.”

Abdulrahman Buba Kwacam da ke jagorantar ƙungiyar raya arewa maso gabar ya zayyana matasan da su ka kutso zanga-zanga da arnatar da dukiyar al’umma da zama sashen matsalar ƙasa.

A na su angaren shugabar ƙungiyar mata na Jamhuriyar Nijar mazauna Nijeriya Dokta Aminatu Abdulkarim ta nesanta ’yan ƙungiyar da shiga zanga-zanga.

Rundunar ‘yan sanda ta musanta kashe mutum 13 da ƙungiyar AMNESTY ta ɗora alhaki kan jami’an tsaro, inda ta ce mutum 7 ne su ka mutu a zanga-zangar ta sanadiyyar bom bin Boko Haram, harbi daga dan banga da takewa da mota da wani mai ganganci ya yi.

Daga jawabin shugaba Tinubu ba alama ta nesa ko ta kusa da ke nuna dawo da tallafin man fetur da ke kan gaba a buƙatun matasan.

Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce bai samu lodin motoci 20 ɗauke da shinkafa da gwamnatin tarayya ta turawa dukkan jihohi ba.

Inuwa Yahaya wanda ya maimaita hakan a taro da ƙungiyar ƙwadago bayan fara zanga-zangar yaƙi da yunwa, ya buƙaci kwantar da hankali don gwamnatin sa zata ɗau matakan tallafawa al’umma kamar yadda ya ce ta yi a baya.

Gwamnan ya zaga ya duba wajajen da ata gari daga ‘yan zanga-zangar su ka lalata da sace kaya, ya umurci ma’aikatar ayyuka ta duba adadin arnar da a ka yi da zummar ba da tallafi.

Da ya ke martani ministan labaru Muhammad Idris ya nuna mamakin kalaman gwamna Yahaya na rashin samun kason buhunan shinkafar.

Hukumar shige da fice ta Nijeriya ta bayyana cewa ta gano da kuma zuba ido kan masu ɗaukar nauyin zanga-zanga a Nijeriya.

Shugabar hukumar Kemi Nandap ta bayyana haka a taron manema labaru na haɗin guiwa da sauran shugabannin tsaro a helkwatar tsaro.

Nandap ta ce mutanen na ƙasashen waje ne kuma da zarar sun nemi shigowa Nijeriya za a cafke su.

Hakanan jami’an tsaron sun ƙara da cewa an rufe asusun ajiyar bankunan Nijeriya na mutanen da yawanci su ke ƙetare.

A na cigaba da neman matasan da su ka gudanar da zanga-zanga da ta haɗa da arnata kayan al’umma.

Yayin da wasu matasan su ka gudanar da zanga-zangar cikin natsuwa, an samu wasu da su ka yi amfani da damar wajen sace dukiyar jama’a.

Kamen ya shafi jihohi da su ka haɗa da Kaduna, Kano da Gombe inda wasu ma matasan da a ka kama tuni an tura su gidan yari.

Har yanzu wasu daga jihohin da zanga-zangar ta gudana na cikin yanayin dokar hana yawo.

Kammalawa;

Sabon salon da zanga-zangar yaƙi da ƙuncin rayuwa da wasu matasan Nijeriya ke yi ta hanyar daga tutar ƙasar Rasha na jan hankalin masana kimiyyar siyasa da diflomasiyya.

Wannan ya biyo bayan matsayar babban hafsan tsaro Janar Christopher Musa da ya zaiyana hakan da cin amanar kasa.

Duk da Janar Musa bayan ganawar hafsoshin tsaro da shugaba Tinubu bai bayyana waɗanda gwamnati ke zargi da ɗaukar nauyin ninka tutocin ba, ya nuna soja ka iya shiga lamarin baya ga matakan ‘yan sanda.

Ganin matasa a Kano, Kaduna da wasu sassa ɗauke da tutar Rasha ya kawo neman bahasi inda a ka ji su na gayatar soja su kare ragamar mulki.

Masanin kimiyyar siyasa a jami’ar Bayero Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa ya baiyana nazarin dalilan daga tutar ciki da kin jinin hukumar lamunin duniya IMF da bankin duniya da kuma lura da yanda wasu ƙasashen Afurka ta yamma su ka yi bayan juyin mulkin soja.

Shugaban gamayyar ƙungiyoyin arewa Jamilu Aliyu Charanci ya ba wa gwamnatin shawarar daukar matakan sauƙin rayuwa don rage wannan bore da ke nuna gayyatar juyin juya hali.

Har ila yau, Dokta Sa’idu Dukawa ya nuna kyautatuwar gano masu ɗaukar nauyin tutocin maimakon dirar mikiya kan matasa da ba mamaki ba su lura da girman matakin da su ka ɗauka ba.

Haƙiƙa dokar hana yawo a wasu daga jihohin  da zanga-zanga ta shafa ta rage kaifin tunzurin duk da matasa musamman a Abuja sun lashi takobin cigaba har sai sun cika kwana 10.

By ukarofi