
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ofishin kula da asusun bada aron kuɗi ga ɗalibai a Nijeriya, NELFUND ya gargaɗi al’umma kan wani shafin damfara da ake amfani da shi da sunan hanyar ɗaukar nauyin karatun ɗalibai a kasashen waje wanda ɗauke da suna da kuma bajinsa.
Jami’in hulɗa da jama’a na ofishin, Mista Nasir Oyitogo ya faɗi hakan wa manema labarai a Abuja inda ya ce ana yaɗa shafin ne ta kafar facebook wanda ya ke kai mutane zuwa ga asalin adireshin mai suna ‘labari.com.ng’.
Ya ce, NELFUND bai da wata alaƙa da wannan shafi ta kusa ko ta nesa, ya na mai cewa an yi haka don ake damfarar ɗalibai da sunansu, saboda da haka ya ke kira ga al’umma da a ƙaurace ma sa.
Ya kuma ce, sun miƙa batun zuwa ga hukumomin da lamarin ya shafa domin gudanar da bincike da yin hukunci akan sa.
A yayin haka ne Jami’ar Ibadan ta jihar Oyo ta ce, ta karɓi Naira biliyan 201,114,650 daga NELFUND ga ɗalibai 1,370 na makarantar don karatun zangon 2023/2024 kamar yadda Daraktar hulɗa da jama’a ta Jami’ar, Joke Akinpelu ta bayyana wa ‘News Agency Nigeria’.
Za a bayar da kuɗin ne ga ɗaliban da aka tabbatar da su daga cikin waɗanda su ka cike ƙa’idojin neman aron kuɗin.
