Da Ɗumi-Ɗumi: An dakatar da shafin X na EFCC kan kutsen ƴan damfara

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

X wanda aka fi sani da ‘Twitter’, an dakatar da shafin na hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati, EFCC ne sakamakon barazanar kutse da ƴan damfara (yahoo boys) suka yi wa shafin.

Hakan na zuwa ne bayan da aka yi zargin cewa EFCC ta sha alwashin ɗaukar mataki kan masu taka doka ta kafafen sada zumunta.

Tun ranar 12 ga watan Agusta ne shafin wanda ke da mabiya miliyan 2.2 ya fara samun tangarɗa inda ya daina buɗewa tare da rubuta ‘Account Suspended’ a safiyar ranar Alhamis.

Saidai, shafukan hukumar na facebook da Instagram su na aiki kamar yadda aka saba.

Mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale ya tabbatar da cewa tsawon kwana uku kenan shafin bai aiki, ya na mai cewa hukumar gudanarwa ta na cigaba da ƙoƙarin ganin ya dawo cigaba da aiki kamar yadda aka saba ganin sa.

EFCC ta shiga gudanar da bincike akan waɗanda ke satar dukiyar al’umma ta yanar gizo inda a watannin baya ne ta yi ta kai samame a otal-otal da wasu yankuna na jami’o’i a faɗin Nijeriya.

By Babaji