
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Ali Modu Sheriff ya ƙaryata rahoton da ke cewa ya zargi Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima da kafa ƙungiyar Boko Haram.
An ga yadda wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta ya yi ikirarin cewa Ali Modu Sheriff ya fito ya ce, “Ba ni ba ne, Shettima ne ya ƙirƙiri Boko Haram.”
Jaridar The Cable ta bayyana cewa a karon farko da aka wallafa wannan rahoto shi ne a watan Agustan shekarar 2016, kamar yadda wani bincikenta ya nuna.
Ali Modu Sherrif ya bayyana wannan labari da ake yaɗawa a matsayin ƙarya, makirci kuma wanda aka ƙirƙira domin haɗa fitina.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Modu Sheriff ya ce labarin ba gaskiya ba ne saidai abu ne da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al’umma da ƙoƙarin ta da rikicin siyasa.
Tsohon gwamnan Borno ya bayyana cewa bai taɓa yin wata hira ko ya magana da ɗan jarida akan wannan batu ba, yana mai cewa an shirya wannan labari ne domin ɓata masa suna.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Wannan rahoto cike yake da yaudara kuma ba shi da kusanci da gaskiya, sannan labarin babban haɗari ne ga zaman lafiya da kwanciyar hankali, musamman ganin irin rawar da Sanata Sheriff ya taka wajen samar da zaman lafiya a Borno da ma fadin ƙasar nan.”
Kazalika, tsohon gwamnan ya roƙi jama’a da kafafen yaɗa labarai da su yi watsi da labarin, yana mai cewa ya umarci lauyoyinsa su gano duk wanda ke da hannu wajen yaɗa ƙaryar.
A ƙarshe, Sheriff ya jaddada ƙudurinsa na cigaba da bada gudummuwa wajen inganta tsaro, zaman lafiya da dimokuraɗiyya a Nijeriya.
