Ali Nuhu ya jinjina wa cibiyar finafinai bisa inganta sha’anin labaran fim

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Cibiyar Horarwa akan harkar Fina-finai ta ƙasa da ke Jos na cigaba da ƙoƙarin inganta al’amuran da suka shafi labaran fim wajen bada horo ga masu neman ƙwarewa a fannin.

Akan haka ne Darakta Manaja ta Hukumar Fina-finai ta Ƙasa (NFC) kuma babban tauraro a masana’antar Kannywood, Dakta Ali Nuhu ya jinjina mata duba da yadda take haskawa a mataki na ƙasa da ma duniya baki ɗaya.

Da yake jawabi a taron farko na baje kolin fina-finai na haɗin-gwiwa tsakanin Tarayyar Turai (EU) da Cibiyar Fina-finai ta Ƙasa (NFI) a ranar Talata a Jos, Jihar Filato, Ali Nuhu ya jaddada aniyar cibiyar ta cigaba da inganta lamuran masu basira a fannin da matasan Nijeriya wajen ba su horon yin fice a harkar fim.

A cewarsa, NFI za ta yi amfani da fim da al’ada wajen ciyar da harkar labaran fim gaba da fannin ƙirƙira, wanda ɗaya ne daga cikin fannonin tattalin arziƙin ƙasa da suka yi fice a ƙasar.

Saboda haka ne Daraktan ya ce yana da kyau a haɗa hannu da hannu wajen ƙarfafa zaƙaƙuran matasan fim a Nijeriya ta yadda za su bada gagarumar gudumawa ga ci-gaban ƙasa.

Ya kuma yaba wa EU bisa gudumawarta ga sha’anin duba da sanya hannu wajen faɗaɗa ayyukan cibiyar a mataka daban-daban.

By Babaji