
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya samu ƙaruwa ta jika daga ɗaya daga cikin ƴaƴansa mata.
Atiku, wanda ya sanar da haka a shafinsa na X a safiyar yau Alhamis, ya ce an yi wa jaririyar suna Fatima-Huda Sale, wadda ƴar fari ce ga ƴarsa Laila.
Ya kuma ce, da ƴar da mahaifiyarta suna cikin ƙoshin lafiya.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana farin cikinsa ga samun ƙaruwar, inda ya yi mata addu’ar fatan samun tsawon rai mai cike da albarka.
Atiku, wanda aka haifa a ranar 25 ga watan Nuwamban 1946, ya nemi zama shugaban ƙasa har sau shida a Nijeriya.


