
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Masarautar Saudiyya ta naɗa Sheikh Saleh bin Al-Fawzan bin Abdullah Al-Fawzan a matsayin babban mai fatawa na ƙasar.
Sarki Salman na ƙasar ya sanar da haka a shafinsa na Facebook, ranar Laraba.
A cewarsa, Sheikh Al-Fawzan zai kuma yi aiki a matsayin Sugaban Majalisar Manyan Malaman ƙasar, sannan Ministan Ma’aikatar Binciken Malamai da Fatawa.
Hakan na zuwa ne wata guda da tsohon mai fatawa na ƙasar, wato Sheikh Abdulaziz bin Abdullahi bin Mohammed Al Al-Sheikh ya rasu bayan shafe shekaru 82 a duniya.
An haifi Sheikh Abdulaziz ne a Makkah, a watan Nuwamban 1943, wanda ya kasance ɗaya daga cikin malaman da ake girmamawa.
