Majalisar Dokokin Katsina ta amince da gina dam a Matazu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta amince da gina Dam a garin Unguwar Mai Yaji a mazaɓar Karaduwa a ƙaramar hukumar Matazu.

A zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar Rt.Hon.Nasir Yahaya Daura, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Matazu Hon. Ibrahim Dikko ya gabatar da ƙudurin akan a gina Dam a garin Unguwan Mai Yaji a mazaɓar Karaduwa a ƙaramar hukumar Matazu.

Ya bayyana cewa samar da madatsar ruwa a wannan wuri zai taimaka wajen noman rani da wadata al’ummar Mai Yaji da sauran garuruwan yankin da ruwan sha.

Haka zalika majalisar ta amince da gyaran hanya da da ta tashi daga Birchi zuwa Dan Kalgo ta miƙe har Dan Gabaci zuwa Rawayau, ta ƙare a ƙaramar hukumar Charanchi duk a ƙaramar hukumar Kurfi.

Ɗan Majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar kurfi Hon. Zaharraddeen Usman Sani ya gabatar da ƙuduri a kan gyaran hanyar da yace yana da muhimmanci wajen alummar waɗannan ƙauyuka “domin yawancin su manoma ne,”Hon Usman ya ce.

Ƙudurin ya samu cikakken goyon baya daga sauran ‘yan majalisar, Kakakin majalisar ya bada umarnin a tura wannan ƙuduri zuwa ɓangaren zartaswa domin ayi duba akai.

By ukarofi