Allah ne kaɗai ya san irin gudunmawar da Marigayi Aminu Ɗantata ya bai wa Musulunci – JIBWIS Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙungiyar Izalatul Bidi’a wa Ikamatul sunnah reshen Jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan ya sanar da haka lokacin da ya ke miƙa ta’aziyar rasuwar Alhaji Aminu Ɗantata.

Ya ce a iya sanin sa babu wani a duniya da ya san iya adadin gudummawar da hamshaƙin ɗan kasuwa marigayi Aminu Ɗantata ya baiwa addinin Musulunci.

Haka kuma ya zuwa yanzu a cewar Sheikh Yakubu Musa Hassan babu wani hamshaƙin ɗan kasuwa da ya sadaukar da rayuwar sa da dukiyar sa wajen ɗaukaka addini musulunci.

“Marigayi Aminu Ɗantata mutum ne da yayi ta burin saduwa da Allah kuma ya cika masa burin sa,”inji Sheikh Yakubu Musa Hassan.

Ya ce ba a sami ɗan kasa da ya rasu,ƙasa ta girgiza irin wannan wannan bawan Allah ba.

Ya bayyana rasuwar sa a matsayin babbar rashi ba ga al’ummar kano ko Nijeriya ba rana da sauran al’ummar musulmi na duniya baki ɗaya.

“Kalmomi na yabo da addu’a da ake yi masa,ana kyautata zaton samun nasarar saduwa da Allah,”inji Sheikh Musa Hassan

Sheikh Yakubu Musa yayi addu’ar Allah masa gafara,yafe masa kurakuransa ya shiryar da zuri’arsa ya haɗa Kawunan su da son juna da ƙaunar addini.

Yayi kira ga al’ummar musulmi masu hali da su ɗauki darasi a gare sa , “su san cewa dukan abinda ya bari a duniya bana sa bane,abinda kawai nasa shine abinda ya kashe wajen raya addinin Musulunci,”Inji Sheikh Yakubu Musa.

Haka kuma ya jawo hankalin wanda Allah ya wadata, Allah ya wadata su ba domin ƙarfin su ba ko dabarar su domin haka suyi ƙoƙari a koda yaushe suna fidda na Allah cikin arzikin da Allah yayi masu.

By ukarofi