Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Dubban al’ummar Musulmi sun gudanar da addu’o’i na musamman na yaƙi da yunwa da wahala da kuma rashin shugabanci nagari a wurare da dama a jihar Kano.
An ruwaito cewa an gudanar da zaman addu’o’i ne domin kawo ƙarshen zanga-zangar adawa da wahalhalun da ƙasar ke fama da shi na tsawon kwanaki 10 na #EndBadGovernance.
A Kano, tun da farko masu gudanar da sallar sun sanar da cewa za a gudanar da taron a masallacin Isyaka Rabi’u, Goron Dutse da sauran wurare da ke faɗin ƙananan hukumomin jihar 44 a ranar Asabar ɗin da ta gabata.
Sai dai a jajibirin taron, ɗaya daga cikin waɗanda suka shirya taron, Mubarak Ibrahim, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa an raba taron addu’o’in domin kaucewa kutsawar ‘yan daba a cikin taron.
