Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Mai Bawa Shugaban ƙasa Bola Tinubu shawara na musamman kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa hauhawar farashin kayan abinci yana raguwa.
Onanuga ya bayyana cewa farashin doya da tumatur da sauran kayan abinci na raguwa matuƙa.
A yayin da wallafa a shafinsa na ɗ, ya rubuta cewa, “Farashin abinci yana saukowa yayin da farashin doya, tumatir ya ragu sosai.”
Ya mayar da martani ne kan wani rahoto da ke cewa farashin kwandon tumatir ya ragu.
Rahoton ya ce, a halin yanzu ana sayar da babban kwandon tumatur a kasuwar Ketu kan kimanin Naira 55,000 zuwa Naira 60,000 – ya ragu da Naira 150,000 a watannin baya.
Ya ce, a yanzu ana sayar da babban kwandon barkonon a kan kuɗi naira 25,000, idan aka kwatanta da naira 55,000 a kwanakin baya.
