Gwamnatin Tinubu ta biya albashin wata 45 da ake bi lokacin Buhari

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ƙarshe dai gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta biya mafi ƙarancin albashi na watanni 45 da Ma’aikatan Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya NiMet ke bin gwamnatin da ta shuɗe.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 12 ga watan Agusta, 2024, mai ɗauke da sa hannun sakataren kwamitin haɗin gwiwa na NiMet, Okechukwu Nwokoro, a ranar Litinin.

Bashin da ba a biya ba, wanda ya samo asali tun daga shekarar 2019 – a lokacin gwamnatin tsohon shugaban aasa Muhammadu Buhari – ya kasance tushen tashin hankali tsakanin hukumar NiMet da ma’aikatanta, wanda ya haifar da rikici da ƙungiyoyin ƙwadago akai-akai.

A farkon wannan shekarar dai lamarin ya kusa ƙara ƙamari zuwa yajin aiki, domin ƙungiyoyin sun shirya fara yajin aikin ne a ranar Litinin 20 ga watan Mayun 2024. Sai dai kuma an daƙile yajin aikin bayan da kwamitin da ke kula da harkokin sufurin jiragen sama da majalisar wakilai suka shiga tsakani.

An dai cimma matsaya ne a ranar Lahadi, 19 ga watan Mayu, 2024, a wani zama na musamman da kwamitin majalisar kan harkokin fasahar jiragen sama, ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar, Abiodun Akinlade, ya shirya tare da wakilan hukumar NiMet da wakilanta.

Sanarwar ta ce, Babban Darakta kuma Babban Jami’in Kamfanin NiMet, Farfesa Charles Anosike, ya bayyana godiyarsa ga Tinubu kan yadda ya ba da izinin biyan bashin.

By ukarofi