Ambaliya: Ɗan Majalisa ya shige wa mazaɓarsa gaba wajen samun tallafi

Daga WAKILIN MU

Ɗan Majalisar Wakilai ta Ƙasa Hon. Nicholas Ossai na jam’iyyar PDP daga jihar Delta, ya yi sanadin rabon tallafin kayayyaki da dama da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 30 ga jama’ar da ambaliya ta shafa gundumar Ndokwa/Ukwuani da ke jihar.

Hon. Ossai ya ce Hukumar Bada Gajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ce ta bada tallafin da aka rabar wa waɗanda lamarin ya shafa.

A bayanin da ya yi Lahadin da ta gabata, ɗan majalisar ya ce kayayyakin tallafin da aka rabar sun haɗa da kwanon rufi, ƙusoshi, silin, siminti, katifu, hidan sauro, barguna, kayan abinci da dai sauransu.

Yayin rabon kayayyakin Ossai ya yaba wa hukumar NEMA bisa amsa buƙatar bada tallafin da ta yi duk da ɗimbin buƙatun da ke jibge a gabanta. Tare da shan alwashin zai ci gaba da yin dukkan mai yiwuwa wajen kyautata wa mazaɓarsa a matsayinsa na wakilin yankin.

Ya ce, “Zan yi amfani da damar da nake da ita wajen yin abubuwan da za su ja hankalin gwamnati da hukumomi wajen aiwatar da ayyukan cigaban a yankinmu.”

Daga nan, Ossai ya nuna tausayawarsa tare da jajanta wa waɗanda ibtila’in ambaliyar ta shafa inda suka tafka ɗimbin hasara.