Ambaliya ta raba ahali 120 da matsugunansu a Jigawa

Rahotanni daga Unguwar Tsallake da ke yankin ƙaramar hukumar Guri a jihar Jigawa, sun tabbatar da kimanin ahali 120 ne suka rasa matsugunansu biyo bayan ambaliyar ruwan da ta auku sakamakon ruwan sama mai yawa da aka samu a yankin.

Jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar, Alhaji Sunusi Doro, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ran Asabar cewa, ibtila’in ya faru ne ta dalilin mamakon ruwan sama a Laraba da Alhamis da suka gabata.

Doro ya ce ambaliyar ta mamaye sama da gidaje 120 wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa matsuguni ga mutane da dama.

A cewar jami’in, “Galibin waɗanda lamarin ya shafa sun koma zama tare da ‘yan’uwa da maƙwabta kasancewar ruwa ya hana su ci gaba da zama a muhallansu.”

Haka nan, ya ce ambaliyar ta haifar wa al’ummar yankin ciska wajen zuwa Babbar Asibitin yankin ta yadda a yanzu dole sai sun shiga ruwa sannan su tsallaka zuwa asibitin.

Doro ya ce, Shugaban Ƙaramar Hukumar, Alhaji Musa Shuaibu, ya janjanta wa waɗanda ibtila’in ya shafa, tare da kira ga Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da ta jihar (SEMA) da su agaza wa jama’ar da ambaliyar ta rutsa da su.

Kazalika, Doro ya ruwaito Shuaibu ya ce kawo yanzu, ƙaramar hukumar ta kashe kimanin N400,000 wajen sayen magani don amfanin ƙauyuka bakwai da lamarin ya shafa da dai sauransu a matsayin gudunmawarta .