Ambaliyar Mokwa: Mutanen da iftila’in ya rutsa da su sun koka da ƙarancin abinci da rashin kyan sansani

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kwanaki uku da aukuwar iftila’in ambaliyar ruwan sama a ƙauyuka da dama na Ƙaramar Hukumar Mokwa a Jihar Neja, mutanen da lamarin ya shafa sun koka game da halin da suka tsinci kawunansu a ciki a sansanonin da aka ware musu.

Sun bayyana cewa, ba su da wadatattun abinci da kuma ingancin wajen zama a wuraren da aka ba su mafaka.

Da dama daga cikin waɗanda iftila’in ya ɗaiɗaita sun ce, duk da cewa hukumomi sun ɗauki hotunansu a lokacin da su ke tare da kayan abinci, hakan bai sa an ba su ba.

Ɗaya daga cikin su mai suna Mama Isa, ta bayyana rashin jin daɗinta ga yanayin a inda ta ce su guda 17 ne daga gidan da ta fito, amma yankan biredi da wani ɗan shayi kaɗai aka ba su yayin rabon abinci.

Ta yi kira ga gwamnati da ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi da su riƙa ba su kayan tallafi kai-tsaye ba tare da shiga tsakani ba.

Haka ma wata mai suna Ruƙaiya Usman ta bayyana irin damuwar, inda ta soki adadin abincin da aka raba da cewa babu iyalin da ɗan abinda aka ba su zai wadace shi.

Baya ga ƙarancin abinci, yanayin wajen zaman su a sansanin ba shi da kyau ga lafiyar ɗan-adam, kamar yadda wani Haussaini Muhammad Adam ya bayyana.

Ya kuma ce, babu makewayi da ruwa mai tsafta, sannan mutane suna fama da rashin lafiya.

Bugu da ƙari, wani Ibrahim Abubakar ya shaida wa manema labarai cewa babu hukumomin bada agajin gaggawa a makarantar Firamare ta Kpege, wadda ɗaya ce daga cikin sansanonin da suke zama.

Tsohon mataimakin gwamnan jihar, Ahmed Ketso ya yi kira ga Gwamnatin Jihar da ta Tarayya da su gaggauta kai ɗauki ga mutanen domin kawo ƙarshen raɗaɗin iftila’in da suke fama da shi.

By Babaji