Yunwarka ta mulki ce ba abinci ba – Wike ga Amaechi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Litinin ne Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bada amsa ga kalamai akan yunwa na tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.

A wata hira da manema labarai a Abuja, Wike ya ce Amaechi ba zai iya zama ba mulki ba, sannan kalamansa na yunwa rainin hankali ne ga ƴan Nijeriya.

Ya ce, duk da cewa ya riƙe muƙamai da dama na tsawon sama da shekaru 20, hakan bai sa ya ji shakkar furta cewa yana jin yunwar abinci ba shekara biyu rak ba tare da wani muƙami ba.

Wike da Amaechi ƴan siyasa ne da suka mulki jihar Ribas mai tarin albarkatun mai a yankin Neja-Delta, inda Wike ya karɓi mulki a shekarar 2015 bayan Ameachi ya kammala shekaru takwas da doka ta ba shi dama.

A shekarar 2023 ne Wike ya kammala wa’adin mulkin jihar.

A ranar Juma’a ne a yayin bikin cikarsa shekaru 60 a duniya, Amaechi ya bayyana cewa yana daga cikin masu jin yunwa a Nijeriya kuma hakan zai iya sa ya shiga ɓangaren haɗaka a ƙarƙashin jagorancin Atiku Abubakar domin sauke Tinubu a zaɓen 2027 da ke tafe.

Ministan na Abuja ya ƙara da cewa, a matsayin Amaechi na wanda ya yi Kakakin Majalisar Dokoki ta Ribas tsawon shekaru takwas, sannan ya yi gwamna da minista su ma na shekaru takwas-takwas, bai dace a ji irin kalamandaga bakinsa ba.

Wike ya kuma bayyana takaicinsa game da lamarin tsohon ministan, yana mai cewa ya yi mamaki a ce mutum ya yi bikin zagayowar haihuwarsa da yaɗa ƙarya acikin al’umma.

By Babaji