Ambasada Sharu Mukhtar ya zama sabon Dan Kaden ƙasar Hausa

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, ya naɗa Matawallen Hausawan Afirka, Ambasada Sharu Mukhtar Abdullahi, a matsayin sabon ɗan Kaden ƙasar Hausa.

Sarkin ya bayyana cewa an zaɓi Ambasada Sharu Mukhtar ne bisa la’akari da iliminsa, ƙwarewarsa da kuma gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa rayuwar al’umma da ci gaban ƙasar Hausa.

Ya ƙara da cewa sarautar za ta ba shi damar ci gaba da wayar da kan jama’a da gudanar da ayyukan ilimantarwa da wa’azi a sassa daban-daban na ƙasar Hausa domin inganta zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban al’umma.

Da yake jawabi bayan karɓar sarautar, Ambasada Sharu Mukhtar ya gode wa Sarkin Daura da masarautar bisa wannan karramawa da suka yi masa.

Ya yi alƙawarin amfani da wannan dama wajen ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya tare da ci gaba da wayar da kan jama’a kan muhimmancin gaskiya, riƙon amana, sana’a da kyakkyawar mu’amala a tsakanin al’umma.

Ita ma matar sabon ɗan Kaden ƙasar Hausa, Hajiya Dakta Zurfau Nasiru Musa, ta yaba wa Sarkin Daura da majalisar masarautar bisa wannan karramawa, tare da gode wa dangi, abokai da maƙwabta bisa goyon bayan da suka bayar tun daga tafiyar zuwa Daura har zuwa dawowarsu Kano.

Ta kuma yi addu’ar Allah Ya ba Sarkin Daura da sauran shugabanni hikima da jagoranci nagari.

By ukarofi

Leave a Reply