Amfani da Intanet ya ragu bayan ƙarin ƙuɗin data

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta bayyana cewa, amfani da bayanan intanet ya ragu da terabyte 17,647 daga watan Janairu zuwa Afrilu na shekarar 2025. Wannan na zuwa ne bayan ƙara kuɗin sabis na sadarwa da kashi 50 cikin 100, wanda ya sa farashin 1GB na data ya ƙaru daga N287.50 zuwa N431.25.

A cewar ƙididdigar masana’antu da NCC ta fitar, amfani da intanet ya faɗi daga 1,000,930.60 terabytes a Janairu zuwa 983,283.43 terabytes a Afrilu. An fi jin tasirin ƙarin kuɗin ne a watan Fabrairu, inda amfani ya faɗi zuwa 893,054.80 terabytes, kafin ya ɗan farfaɗo zuwa 995,876.10 terabytes a Maris, amma ya sake raguwa a Afrilu.

Adadin masu amfani da intanet ma bai tsira ba, inda daga mutum 142,161,409 a Janairu suka ragu zuwa 141,985,207 a Afrilu. A watan Fabrairu kaɗai, an rasa fiye da masu amfani 900,000 sakamakon ƙarin kuɗin da kuma wahalar tattalin arziki.

Wannan na nuna yadda ƙarin farashin sabis ke jefa jama’a cikin matsin lamba wajen cin gajiyar fasahar sadarwa.

Bugu da ƙari, an tabbatar da cewa sabuwar dokar haraji da shugaban ƙasa ya amince da ita za ta sake kara wa ‘yan Najeriya nauyi. Wannan dokar harajin da majalisar dattawa ta amince da ita a watan Mayu na 2025, ta dawo da harajin kashi biyar cikin 100 kan sabis na sadarwa, ciki har da kira, sakon tes da data, abinda masana ke cewa zai ƙara tsadar rayuwa da hana ci gaban shiga fasaha.

Kamfanonin sadarwa irin su MTN sun bayyana fargaba kan sabon harajin da kuma ƙarin kuɗin da aka yi baya bayan nan.

Duk da MTN ta samu riba mai tsoka a farkon shekarar 2025, kamfanin ya bayyana cewa hakan na da nasaba da ƙarin buƙatar data da kuma farfaɗowar tattalin arziki, amma har yanzu akwai fargabar cewa ƙarin haraji da matsin tattalin arziki zai iya janyo koma baya a ɓangaren sadarwa.

By ukarofi